Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Isra'ila Ta Kame Falasdinawa 350 Da Ke Sallah Masallacin Qudus

  'Yan sandan Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kame Falasdinawa fiye da 350 a wani hari da suka kai cikin Masallacin Al-Aqsa lokacin da ...

 


'Yan sandan Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kame Falasdinawa fiye da 350 a wani hari da suka kai cikin Masallacin Al-Aqsa lokacin da musulmi ke tsaka da sallah. 

Rahotanni sun ce jami’an ‘yan sandan na Haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi yunkurin tarwatsa masu Sallar ne bisa kafa hujja da cewa sun dade a cikin masallacin fiye da wa’adin da aka dibar musu, lamarin da ya sanya Falasdinawa tirjiya domin bayar da kariya ga masallatan.

Bayan kamen da kuma jikkata wasu da dama a harin da haramtacciyar kasar Isra'ila suka kai a daren jiya Talata kari kan hari da jiragen Soji da Isra’ila ta kai kan zirin Gaza, kungiyar Hamas da ke jagorancin yankin ta mayar da martani ta hanyar farmakar Isra’ila da wasu makamai masu linzami.

Dakarun Haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da mamaye gabashin birnin Qudus inda lamarin ke kara zafafa a daidai lokacin da al’ummar musulmi ke azumin watan Ramadana wanda a wannan karon ya zo daidai da wani bikin al’ada na Yahudawa.

Tun farko Hamas ta bukaci al’ummar yankin da su fita su kare masallacin daga Yahudawan kama guri zauna. 

No comments