Fassarar Muhammad A. Abubakar Bayanai na ƙara fitowa kan yadda gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Bello Mohammed Matawalle ya cire kuɗa...
Fassarar Muhammad A. Abubakar
Bayanai na ƙara fitowa kan yadda gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Bello Mohammed Matawalle ya cire kuɗaɗe daga baitul malin jihar a matsayin biyan kuɗaɗen ayyukan da aka yi watsi da su baki daya a faɗin jihar.
Binciken sunayen ‘yan kwangilar ya nuna cewa galibin kamfanonin da aka bai wa ayyukan suna da alaka kai tsaye ko a kaikaice da Gwamna mai barin gado. Kuma a mafi yawan lokuta, ’yan kwangilar ana ba su kwangiloli mabambanta da suka hada da gine-ginen tituna, gina masaukan Gwamna a faɗin kananan hukumomin, da kuma sauran ayyukan da aka yi watsi da su waɗanda suka ci biliyoyin Naira.
Jihar Zamfara ta dade tana cikin labarai marasa daɗi a tsawon shekaru da dama. A baya-bayan nan an samu rahoton yadda ma’aikatan gwamnatin jihar suka yi kukan cewa sun yi bukukuwan Sallah cikin su fanko sakamakon Gwamna Matawalle ya kasa biyansu albashin su na wata-wata.
Ma’aikatan sun zargi Gwamnan da kin amincewa da biyan albashin da gangar saboda ya sha kaye a zaben da ya sake tsayawa takara. Duk da cewa dama jihar ta kasance cikin bakin littafi na rashin biyan albashin ma’aikatanta a lokacin da ya kamata.
Sakamakon binciken da Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta yi ya nuna cewa Zamfara ce jiha mafi karancin ci gaba a ƙasar nan. Binciken da hukumar kididdiga ta yi ya nuna cewa kashi 78 na mazauna jihar talakawa ne.
Wannan jiha ce da ke da matukar bukatar taimakon gwamnati ta hanyar shirye-shiryen da za su kawar da talauci a faɗin jihar. Al’ummar Zamfara na da bukatar saka hannun jarin da zai samar musu da ayyukan yi waɗanda za su magance yawaitar rashin aikin yi musamman ga matasa.
Maimakon mayar da hankali kan ayyukan da za su inganta rayuwar jama’a a Zamfara, gwamnati mai barin gado ta Bello Mohammed Matawalle ta karkata akasarin hankulanta kan ayyukan da talaka ba zai amfana ba waɗanda idan aka fara ake yin watsi da su cikin gaggawa.
Sanin al’umma ne yadda ‘yan kwangila suka yi watsi da aikin gina masaukan Gwamna a faɗin kananan hukumomi 14 na jihar. An fitar da biliyoyin naira daga baitul malin jihar kuma an biya ‘yan kwangilar kuɗaɗen gina masaukan wanda ba a kammala ko kashi 30% ba.
Wannan al’adar ta cin hanci da rashawa ta hanyar fitar da kuɗaɗe domin gudanar da ayyuka marasa amfani ko ayyukan da ba a kammala ba ta ratsa kusan dukkan bangarori, ba wai kawai ga ayyukan gina masaukan Gwamna da yake son yi kadai ba. An samu ƙarin hujjoji kan yadda gwamnatin mai barin gado ta kwashe tare da biyan cikakken kuɗi ga ‘yan kwangila kan ayyukan da ba a aiwatar da su ba ma sam-sam.
Binciken irin waɗannan ayyuka ya bankado yadda Gwamna Matawalle ya karkatar da kuɗaɗen jihar – inda ake biyan ‘yan kwangilar ayyukan da ba a kammala ba.
Gwamnatin jihar Zamfara mai barin gado ta amince da kuɗi naira 593,535,254.00 domin gina hanyar da ta hada Kaiwa zuwa Lamba zuwa Gundumar Gidan Goga dake kan babbar hanyar tarayya ta Kauran Namoda/Shinkafi. Jimillar kuɗi har naira 525,510,516.77 aka saki ga dan kwangilar, MotherCat Nigeria Limited. Kuɗaɗen da ake bin ba shi shi ne 68,024,737.23, amma ba a fara wani aiki ba.
Gwamnatin mai barin gado ta kuma amince da kuɗi naira biliyan 1,875,259,890.00 domin gina titin Danmarke zuwa Kanoma a karamar hukumar Maru. An cire jimillar kuɗi naira 1,567,566,531.65 daga asusun gwamnati, aka kuma mikawa kamfanin kwangilar NAEL BIN HARMAL Hydro Export (NBHH) Nigeria Limited. Kuɗin da ya rage a biya shi ne 307,693,358.35 kuma abin takaici har yanzu ba a fara aikin ba.
Bugu da ƙari, an ba wani ɗan kwangila mai kamfanin Syndicate Construction and Commercial Company LTD kwangilar gina hanyoyi biyu; Titin Maradun zuwa Magami da Faru a karamar hukumar Gwamna Matawalle mai barin gado da kuma gina titin Mada zuwa Wonaka, da kuma hanyar R/Bore. An cire kuɗi naira 3,39,118,189.70 daga baitul malin jihar Zamfara, aka kuma biya a matsayin biyan kuɗin aikin, wanda har yanzu ba a fara ba balle a yi batun kammalawa.
Jimillar kuɗi naira 172,486,489.45 aka mika wa M. Sulaiman Enterprises Limited a matsayin biyan kuɗin da gwamnatin jihar Zamfara ta yi na gina Chediya Ukku – Gidan Mayana – Magama zuwa Tullukawa mai tsayin mita 600 a kan hanyar Anka. Amma ba a ma fara aikin ba.
An bai wa wani dan kwangila mai suna Solid Soils Limited kwangilar gina Kwanar Magarya zuwa Magama zuwa Yanbuki zuwa titin Jibiya. An fitar da jimillar kuɗi naira 929,502,249.04 daga asusun gwamnatin jihar a matsayin biyan kuɗin aikin, duk da haka babu wani abin a nuna.
A karshe, gwamnatin Bello Mohammed Matawalle mai barin gado ta amince da sake gina babban asibitin karamar hukumar Shinkafi tare da kammala shi. An saki jimillar kuɗi naira 2,429,301,036.61 ga dan kwangilar mai kamfanin 180 Circle Construction and Engineering Limited wanda ya kunshi sama da kashi 80% na adadin kuɗin da aka amince da shi na aikin, duk da haka babu wani abu da zai nuna ana aikin.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin ayyukan da aka yi watsi da su da gwamnatin jihar Zamfara mai barin gado ta kammala sakin kuɗaɗensu a matsayin biyan ‘yan kwangilar.
No comments