Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Kungiyar Mawallafa Labarai Ta Zariya Ta Mika Ta’aziyyarta Ga Editan LEADERSHIP Bisa Rasuwar Mahaifinsa

Kungiyar masu wallafa labarai a kafar yanar Gizo da ke garin Zariya cikin jihar Kaduna,(ZOJF) ta mika ta’aziyyarta ga Malam Yusu...


Kungiyar masu wallafa labarai a kafar yanar Gizo da ke garin Zariya cikin jihar Kaduna,(ZOJF) ta mika ta’aziyyarta ga Malam Yusuf Shu’aibu, Editan labarai na jaridar LEADERSHIP Hausa bisa rasuwar mahaifinsa Alhaji Shu’aibu Isma’il.

Alhaji Shu’aibu Isma’il, ya rasu ne a ranar Alhamis, inda tuni aka yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Kungiyar a sakonta na ta’aziyar wanda shugabanta ya rattabawa hannu, Ammar Muhammad Rajab ya nuna kaduwarsa da jin labarin rasuwar ya kuma yi addu’ar samun gafara da Rahama ga marigayin wurin ubangijinsa.

Rajab ya ce, “A madadin iyalai na da ‘ya’yan kungiyar, ina mai mika ta’aziyyar mu zuwa ga abokin aiki Malam Yusuf Shu’aibu, bisa rasuwar mahaifinsa Alhaji Shu’aibu Isma’il.”

Kungiyar ta kuma mika ta’aziyyarta zuwa ga ‘yan uwa da abokan arzikin marigayi Alhaji Shu’aibu Isma’il, inda kungiyar ta yi addu’ar Allah ya yafewa marigayin kura-kuransa ya kuma sa Aljannah Firdaus ce makoma amin.

Rajab ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa Edita Malam Yusuf Shu’aibu da kuma daukacin danginsa kan wannnan babban rashin hakuri, da fatan kuma Allah ya ba su ikon jure rashin.


No comments