Mai tsaron baya na Manchester United Luke Shaw ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa zuwa karin shekaru 4 a nan gaba wadd...
Mai tsaron baya na Manchester United Luke Shaw ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa zuwa karin shekaru 4 a nan gaba wadda za ta kai shi har watan Yunin shekarar 2027.
Sabuwar yarjejeniyar na nuna cewa, Shaw mai shekaru 27 zai samu zama a Old Trafford har fiye da shekaru 10 bayan sayensa daga Southampton a shekarar 2014.
Shaw dan Ingila wanda ya samu cikakkiyar dama karkashin Manaja Erik ten Hag ya haska a fili sau 36 yayinda ya zura kwallo guda ya kuma taimaka aka zura wasu 6, a jawabinsa na sanya hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwnatiragin, ya ce yana cike da murna kwatankwacin shekaru 9 baya da ya isa Old Trafford.
A cewar Shaw a United ne ya samu cikakkiyar damar da kowanne dan wasa ke fata kuma ya samu tarin nasarori.
Shaw wanda zuwa yanzu ya dokawa United wasa 249 ya gamu da matsin lamba a United lokacin jagorancin Jose Mourinho wand aba a kowanne wasa ake amfani da shi ba, sai dai Ole Gunnar Solskjaer da kuma Ten Hag a yanzu, Shaw ya zama dan wasan da ake ganin kafarsa a kusan dukkanin wasannin Manchester United.
No comments