Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Mahaifinmu Jagora ne abin koyi –Iyalan Marigayi Farfesa Idris Abdulkadir

  Marigayi Farfesa Idris Abdulkadir *Rasuwarsa rashi ne babba –Farfesa Ango Abdullahi Daga Danjuma Rabiu Iyalan Marigayi Farfesa Idris Abdul...

 

Marigayi Farfesa Idris Abdulkadir

*Rasuwarsa rashi ne babba –Farfesa Ango Abdullahi

Daga Danjuma Rabiu

Iyalan Marigayi Farfesa Idris Abdulkadir sun bayyana mahaifinsu a matsayin jagora abin koyi. Inda suka ce shi jagora ne da yake bayar da kyawawan shawarwari da za su kai mutum tudun mun tsira. Iyalan sun ce Marigayin shi mutum ne mai gaskiya da adalci ga iyalansa da kuma sauran al’umma baki daya. 

Iyalan sun bayyana hakan ne ta bakin dansa na biyu, Abdulkadir Idris, babban dansa namiji a yayin ziyarar ta’aziyyar da kungiyar mawallafa labarai a yanar gizo na Zariya suka kai musu a gidansu dake GRA Sabon Garin Zariya.  

A ranar Juma'a 15/06/2023 daidai da 23/Ramadan 1444 tawagar kungiyar ‘yan jarida na yanar gizo na Zariya suka kai jajen rashin da aka yi na Farfesa Idris Abdulkadir a gidansa dake GRA a Sabon Garin Zariya. Inda suka suka sami tarbar Babban dansa a maza wato Abdulkadir Idris. 

Bayan gabatar da ta’aziyya daga kungiyar. Jagoran tafiyar, Idris Umar daga Jaridar Leadership Hausa, ya bayyana wannan babban rashi da aka yi a matsayin rashi ne da ya shafi dukkanin al’ummar kasa baki daya. Kuma ya yi addu’ar Allah ya yi masa Rahama. 

A nasa jawabin, Abdulkadir Idris, dan marigayin ya bayyana mahaifin na su a matsayin shugaba kuma jagora abin koyi. 

Ya tabbatar mana da cewa mahaifinsu ya auri mata uku, inda daya ta rasu, amma ya bar mata daya da ‘ya’ya goma wanda ya hada maza hudu da mata shida da kuma jikoki goma sha biyar. 

Sannan ya yi godiya da nuna gamsuwarsa da wannan ziyarar ta’aziyyah da aka kawo musu. 

Daga nan tawagar ta tashi ba ta tsaya ko’ina ba sai gidan tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, kuma shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Magajin Kogin Zazzau, Farfesa Ango Abdullahi domin jajanta masa bisa wannan rashi. 

Tawagar ‘yan jaridar sun jajanta masa bisa rasuwar tsohon shugaban hukumar lura da jami’o’i na kasa, Farfesa Idris Abdulkadir. 

A na shi jawabin, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana rasuwar mamacin a matsayin babban rashin da suka yi sannan ya yi addu’ar Rahama ga mamacin. 

Farfesa Ango Abdullahi. 

A yayin zantawarsa da ‘yan jaridar, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa shi mai kishin arewa ne farko kafin Nijeriya. Sannan ya nusasshe da cewa mafita shi ne a dawo a gyara barnar da kowa ya yi, domin a cewarsa ba yadda za a yi ka bata gidanka ka yi zaton wani ne zai zo ya gyara maka. 

Da yake Magana kan al’ummar Arewa kuwa, ya ce wasu da dama ba su san dalilin da yasa ake zabe ba, inda ya ce ana zabe ne domin a zabo shugabannin nagari da za su kai al’umma tudun mun tsira. Inda ya gargadi al’umma da su kiyayi yin zabe domin kudi, ya ce abin kunya ne mutane su rika zabe ana ba su Taliya da naira dari biyar. 

Sannan ya yi kira ga iyaye da su guhji tura ‘ya’yansu zuwa bara da sunan neman karatu, y ace matukar gwamnati ba ta magance irin wannan dabi’ar ba, to babu ranar da za a samu tsaro a kasarnan. 

Sannan ya kwankwashi ‘yan jarida da su rika fadin gaskiya a yayin gudanar da aikinsu ba tare da tsoro ko shayin ‘yan siyasa ba. 


No comments