Daga Muhammad A. Dalhatu Kwanaki goma sha biyar (15) da sace dalibai a makarantar Sakadaren gwamnati dake Awon a jihar Kaduna, daga karshe...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Kwanaki goma sha biyar (15) da sace dalibai a makarantar Sakadaren gwamnati dake Awon a jihar Kaduna, daga karshe sun samu sun tsere daga hannun masu garkuwa da su. Rahotanni daga hukumar jihar Kaduna ta tabbatar da tserewar daliban kamar yadda majiyarmu ta labarta mana.
Ɗalibai takwas da aka sace daga babbar makarantar sakandaren gwamnati da ke Awon a jihar Kaduna sun samu kuɓuta daga hannun masu garkuwa.
An dai sace ɗaliban ne a ranar 3 ga watan Aprilu a ƙaramar hukumar Kachia da ke jihar.
A cewar majiyoyi, ɗaliban sun samu tserewa daga duhun dajin da ke kusa da iyakar Kaduna zuwa Neja inda aka sace su.
Rahotanni sun ce ɗaliban mata sun yi tafiyar kwanaki har sai da suka samu tsira sannan suka nemi a taimaka musu.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na facebook ya ce sun samu bayanan sirri da suka ankarar da gwamnati cewa ɗaliban sun samu tserewa daga nan ne kuma Gwamna Nasir El Rufai ya bayar da umarnin a kwaso su.
A cewarsa, ƴan bindigar sun yi wa yankin ƙofar rago inda suke laluben ɗaliban, lamarin da ya sa gwamnati ta gaggauta kai wa ɗaliban ɗauki.
Ya ce ɗaliban su takwas tuni aka kwashe su zuwa wajen sojoji inda ake duba lafiyarsu.
Aruwan ya kuma ƙara da cewa gwamna El Rufai ya yaba wa ɗaliban bisa irin namijin ƙoƙarinsu wajen tserewa.
No comments