Manchester United ta kai wasan ƙarshe a gasar kofin FA bayan da ta doke Brighton da ci 7-6 a bugun fenareti, a filin wasa na Wembley. Soll...
Manchester United ta kai wasan ƙarshe a gasar kofin FA bayan da ta doke Brighton da ci 7-6 a bugun fenareti, a filin wasa na Wembley.
Solly March na Brighton ne ɗan wasa ɗaya tilo da ya zubar da bugun fenaretinsa a karawar.
Tun da farko dai an tashi wasan babu ci a mintuna 90 na wasan, inda aka tafi ƙarin lokaci na mituna 30 nan ma babu ci.
A yanzu United za ta kara da makwabciyar Man City, wadda ta doke Sheffield United da ci 3-0 ranar Asabar.
Za dai a buga wasan ƙarshe ranar Asabar Uku ga watan Yuni a filin wada na Wembly.
A ranar Alhamis ne Sevilla ta fitar da United - wadda ke mataki na huɗu a kan teburin Premier - daga gasar Europa League ta bana.
Manchester City a ɗaya ɓangaren - wadda ke mataki na biyu a teburin Premier ta kai wasan dab-da na ƙarshe a gasar Zakarun Turai ta Champions Leageu.
No comments