Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Me Ya Haddasa Kasawar Shanun Fulani 34 A Ƙaramar Hukumar Lere?

  Daga Aliyu Ishaq Saminaka A yammacin ranar Alhamis 27 ga watan Afrilun 2023, al’ummar da suke maƙwabtaka gadar Lere na jihar K...

 
Daga Aliyu Ishaq Saminaka

A yammacin ranar Alhamis 27 ga watan Afrilun 2023, al’ummar da suke maƙwabtaka gadar Lere na jihar Kaduna sun gamu da Iftila’in kasawar Shanu guda 34 inda aka yi nasarar yanka guda Ashirin da bakwai (27), guda ɗaya (1) ta mutu a ciki inda aka garzaya da Shanu shida (6) domin yi musu magani.

Lamarin ya faru ne biyo bayan fitowar shanun daga wata gonar Lambu bayan an cire amfanin da yake cikinta. Fulanin sun zargi da guba aka sanyawa Shanun su  a cikin gonar.  

Mun samu zantawa da me dabbobin kuma shi ne Kansilar Gundumar Sabon Birni a ƙaramar hukumar Lere. Hon. Maiwada Suleiman, inda ya ce; “Yaranmu sun shiga da shanun mu cikin wannan gonar bisa izininsa (me gonar) inda ya nemi mu siya gonan ya faɗi abin da zamu ba shi har mun yi ciniki mun biya kafin mu shiga da shanun amma da shanun suka shiga, suka ci ciyawar sai wani abu ya faru daban. Wanda ba mu yi tsammani ba. A halin yanzu mun sanar da Hukumar Ƴan sanda na ƙaramar hukumar Lere. Sun kama me gonar tare da mai gadinta domin gudanar da bincike. Haka zalika, muna sanar da hukumar kiwon lafiya na Dabbobi domin gano wani irin nau’in guba suka ci."

Shugaban Fulani makiyaya reshen Arewa ta tsakiya, Alhaji Gidaɗo Bebeji ya yi kira da gwamnati da shugabannin al'umma dangane da yanayin da ake ƙoƙarin shiga, inda ya ce; bai kamata irin wannan al'amari yana faruwa a tsakaninmu ba! Domin Fulani da Manoma ba abokan gaba bane. 

Daga karshe sun kara yin kira da a yi musu adalci.

No comments