Daga Fatima Idris, Zariya Mutane 700 ne suka amfana da tallafi daga Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. ...
Daga Fatima Idris, Zariya
Mutane 700 ne suka amfana da tallafi daga Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.
Tallafin da Dan majalisa yake bayarwa ya taba bangarori da dama na rayuwar al'ummar karamar hukumarsa ta Sabon Gari.
Baya ga tallafin abinci da Dan majalisa ya bayar ga daruruwan jama'a tuni ya shirya taron koyar da sana'ar dogaro da kai ga daruruwan jama'arsa.
Wakiliyarmu ta ziyarci dukkan bangaren da ake bayar da horon domin tabbatar wa da idonta abin dake gudana a wajen.
Wuraren da ake bayar da horar ga daruruwan al'ummar ta karamar hukumar guda biyu ne kuma duk cike yake da mutane. Bisa haka ne muka nemi jin ta bakin mai taimakawa Dan majalisar a bangaren harkar gudanarwa.
Kwamared Ado ya bayyana dukkan abubuwan da Dan majalisan ya gudanar a ‘yan kwanakin nan a matsayin tallafi a karkashin Jam’iyyarsu ta APC.
Ado ya kara da cewa a yanzu haka mutane 700 ake bai wa horo maza da mata da samari da harda tsofafi dukkansu ana ba su horo ne na koyon kananan-kananan sana'ar kamar yadda za su iya hada Alkaki na zamani ko yadda za su hada kek na zamani kuma idan sun kammala samun horon Dan majalisa zai ba su naira dubu ashirin da biyar (N25, 000) ga ko wanne da ya sami horon domin yin jari.
Mataimaki na musamman ya kara da cewa satin daya gabata Dan majalisar ya bayar da buhun shinkafa manya da kanana guda (1, 500) ga jama'a. Haka zalika ya bayar da tallafin buhun Gero guda 700 ga jama'a domin samun albarka.
Ado ya tabbatar da cewa duk a satin da ya gabata Dan majalisa Garba Datti Muhammad Babawo ya sayawa hukumar kula da hadura hanya ta kasa Mota babba ta daukar marasa lafiya. Kuma yanzu haka ya kawo wa dukkan gundumomi 11da ake da su a fadin karamar hukumar Sabon Gari fitillar Sola mai haske titi guda 100.
Ya ce abin mamaki da alfahari shi ne da yawan aikin da shi Dan majalisan ya yi a yanzu ya yi sune bayan an shelanta ya fadi zabe duk da suna kalubalantar sakamakon zaben a matsayin an tafka magudi ne tsagwaro, in ji shi.
Tuni Ado ya yi godiya ga Allah bisa kokarin da Dan majalisar ke yi a fadin karamar hukumar a lokacin baya da kuma yanzu.
Malama Rukayya Muhammad daga Anguwar Gabas Sabon gari tana daga cikin matan da suka sami tallafin bisa haka ta ce su har yanzu Honorabul Babawo shi ne Dan majalisar su kuma ta ce t aji dadin horon da ta samu kuma za ta yi amfani da ilmin da ta samu kuma za su amfani da jarin da aka bata.
Muhammad Sani daga gundumar Basawa shima ya sami tallafin kuma ya yi wa Dan majalisar fatan alheri da rokon Allah ya bashi nasara a duk inda ya sa gabansa.
Alhaji Hasan Abdul Sakatare ne na karamar hukumar Sabon Gari shima ya ziyarci wajen da ake horas da jama'ar bisa yadda ya ga komai na tafiya ne ya yi wa Dan majalisar ta su fatan alheri tare da jinjina ga ayyukansa na alheri kuma ya yi kira ga mahalarta taro da su yi amfani da abin da suka samu a hanya ta gari.
Zuwa yanzu bincike ya nuna cewa jama’a sun fara kewar Dan majalisar tare da yi masa fatan Allah ya dawo da shi kujeransa su ci gaba da samun irin wannan gagarumin taimako.
No comments