Daga Muhammad A. Abubakar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki jama’ar kasar da su masa aikin gafara idan ya saba musu a cikin shekaru 8 ...
Daga Muhammad A. Abubakar
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki jama’ar kasar da su masa aikin gafara idan ya saba musu a cikin shekaru 8 da ya yi yana mulkinsa wanda ke kawo karshe a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Buhari ya nemi gafarar ce lokacin da mazauna birnin Abuja suka kai masa ziyarar Barka da Sallah a fadar gwamnati, inda ya bukaci yafiya idan ya sabawa wani yayin gudanar da aikinsa.
Shugaban ya kuma godewa jama’ar kasar saboda yadda suka yi ta jurewa gwamnatinsa a shekarun da suka gabata, inda ya ce ziyarar Barka da Sallar ta bashi damar gabatar musu da godiyarsa da kuma yi musu ban kwana ganin cewar a watan gobe zai sauka daga karagar mulki.
Buhari ya shaidawa mazauna Abujan cewar ya shirya yadda zai nesanta kansa da birnin da zarar ya bar karagar mulki, saboda burinsa na mulki ya cika, abin da zai bashi damar komawa mahaifarsa domin yin ritaya.
Shugaban ya ce Allah ya bashi gagarumar dama wajen yi masa gwamna da minista da kuma shugaban kasa har sau biyu, saboda haka ya gode masa domin cimma burinsa na rayuwa.
No comments