Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Na Yi Farin Ciki Da Tarbar Da Aka Nuna Min - Tinubu

  Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi farin cikin komawa ƙasar bayan hutun mako biyar da ya yi a birnin Paris na ...

 


Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya yi farin cikin komawa ƙasar bayan hutun mako biyar da ya yi a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa Tuwita, Bola Tinubu ya ce ya yi matuƙar farin ciki da annashuwa kan irin gagarumar tarbar da aka yi masa a lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Abuja babban birnin ƙasar.

Zaɓaɓɓen shugaban ya kuma gode wa ɗimbim masiya da magoya bayansa kan irin ƙaunar da ya ce suna nuna masa.

Ya ƙara da cewa yana nan a kan alƙawarin da ya ɗauka na samar da sabuwar Najeriya.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya kuma ce yana cikin ƙoshin lafiya saɓanin jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana cikin halin rashin lafiya.

No comments