Newcastle United ta yi wa Tottenham Hotspur kaca-kaca da ƙwallaye biyar cikin mintuna 21 na farkon fara wasa, a karawar da ake kallo a mat...
Newcastle United ta yi wa Tottenham Hotspur kaca-kaca da ƙwallaye biyar cikin mintuna 21 na farkon fara wasa, a karawar da ake kallo a matsayin faɗan ƙwatar gurɓi a cikin huɗun farko na saman taburin Premier.
Jacob Murphy da Alexander Isak kowannensu ya ci ƙwallo biyu a wasan, yayin da Joelinton ya ƙara ta biyar kafin a je hutun rabin lokaci.
Bayan komawa hutun rabin lokaci ne Harry Kane ya zare kwallo ɗaya, sai dai ba a jima ba Callum Wilson ya kara wa Newcastle ƙwallonta ta shida a karawar jim kaɗan bayan shigarsa wasan.
Wannan rashin nasara babbar koma-baya ce ga Tottenham wadda ke ƙoƙarin shiga sahun huɗun farko a gasar ta Premier domin samun gurbin buga gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.
No comments