Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Rikicin Sudan Ya Hana 'Yan Nijeriya Komawa Gida Daga Umara

  Rahotanni sun ce daruruwan 'yan Najeriya da suka je aikin Umara Saudiyya na makale a kasar bisa rashin samun jirgin da zai mayar da su...

 


Rahotanni sun ce daruruwan 'yan Najeriya da suka je aikin Umara Saudiyya na makale a kasar bisa rashin samun jirgin da zai mayar da su gida. 

Jaridar Daily Trust da bayyana cewa wadanda lamarin ya fi shafa su ne wadanda suka yi amfani da Badr Airline lokacin tafiya, wani kamfanin jirgin kasar Sudan da a baya-bayan nan ya dakatar da ayyukansa sakamakon yakin Sudan.

Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne bama-bamai suka tarwatsa jiragen kamfanin biyu a birnin Khartoum. 

Yayin da sauran jirage suka kauracewa keta sararin samaniyan Sudan zuwa Najeriya sabida dalilan tsaro, Badr Airline kuwa dakatar da aiki ya yi baki daya. 

Daily Trust ta ce wani fasinja da ke cikin wadanda suka makale a kasa ya sanar da ita cewa an bukaci duk wani fasinjan da jirgin Sudan ta kaai shi ya nemi wata mafita.

Bayanai sun ce wanda suka koma ta wasu kamfanonin jirage sai da suka biya wasu karin kudade domin jirage basu bin ta sararin samaniyan Sudan.

No comments