Daga Yusuf Abubakar Babale Sarkin Gwantu (Mai Gwantu) da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, Malam Balarabe Abdullahi Karma, ya nada ta...
Daga Yusuf Abubakar Babale
Sarkin Gwantu (Mai Gwantu) da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, Malam Balarabe Abdullahi Karma, ya nada tare da bai wa Alhaji Muhammad Umar Intu sarautar Magajin garin Gwantu,
Mai Gwantu har wala yau ya kuma ba da sanarwar rusa a nan take, dukkannin wasu Sarautu na gargajiya da aka bai wa dukkan ‘ya’yan masarautar maza da mata a karkashin masarautar Numana.
Alhaji Karma wanda ya yi magana jim kadan bayan nadin Sarautar Magajin gari a fadarsa da ke Gwantu a ranar Juma’a ya ce, “na rushe dukkanin masu rike da sarautun gargajiya da aka ba wa ‘ya’yan masarauta ta maza da mata a karkashin tsohuwar masarautar Numana”.
Haka kuma Sarkin ya yi kira ga dukkan fitattun ‘ya’yan masarautar maza da mata masu sha’awar kwatowa ko neman sarautar gidansu ko ta Kakanninsu da su fito domin neman wannan mukami, inda duk wanda ya cancanta za a tantance shi a kuma nada masa wannan sarauta bisa cancanta.
Ya kuma bayyana shirin majalisar masarautar na ba da sabbin mukamai ga duk masu sha'awa, amma wadanda suka cancanta daga maza da mata na masarautar.
Da yake jawabi tun da farko, Mai Gwantu ya ce a matsayinsa na Magajin gari mai yawan al’adu da addinai da kabilu daban-daban a karamar hukumar, dole ne sabon Magajin Garin ya rungumi kowa tare da yin aiki da kowa ba tare da la’akari da addini ko al’ada ko akida ba.
Ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar Masarautar da su rungumi zaman lafiya da hadin kai a kodayaushe, wanda ya jaddada cewa shi ne kawai mafita ga cimma nasara da zaman tare da ci gaban kasa da jiha da kuma karamar hukumar.
No comments