Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shaikh Ibraheen Zakzaky Ya Raba Kayan Abincin Watan Ramadan A Bana

Daga Aba Sajjadi Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; kamar kowacce shekara, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky na raba kayan ab...


Daga Aba Sajjadi

Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; kamar kowacce shekara, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky na raba kayan abinci ga mabuƙata a lokacin watan Ramadan. Kuma wannan aikin ya kwashe shekaru yana yinsa. Domin duk shekara yana rabawa bayin Allah abincin da suke amfana da shi a lokacin watan Ramadan mai alfarma.

A yau Laraba bakwai (7) ga watan Ramadan 1444 Hijiriyya wanda ya yi daidai da 29/03/2023 ne, Shaikh Zakzaky daga inda yake ya fara raba kayan abinci ga mabuƙata na watan Ramadan kamar yadda ya saba yi tsawon shekaru.

Abincin da aka raba sun haÉ—a da: Shinkafa, Gero, Masara, Dawa da kuma Suga da ma sauran su. Wannan rabon da Shaikh Zakzaky ke yi ba sabon abu bane ga mutanen garin Zariya da kewaye. Domin an saba yinsa. 

Shaikh Zakzaky a ƙarshe ya yi fatan alheri ga al'ummar Annabi Muhammad (S.A) dangane da shigowar watan Ramadan mai alfarma.


No comments