Wasu daga cikin mahalarta taron Gidan Kanawan Likoro Daga Ammar M. Rajab Kamar yadda suka saba a duk shekara, Gidauniyyar Gidan Kanawan Li...
![]() |
Wasu daga cikin mahalarta taron Gidan Kanawan Likoro |
Daga Ammar M. Rajab
Kamar
yadda suka saba a duk shekara, Gidauniyyar Gidan Kanawan Likoro na shirya taro
domin sada zumuncin dake tsakaninsu. A bana ma gidauniyyar ba ta yi kasa a
guiwa ba, sun shirya irin wannan taro a ranar Litinin 24 ga watan Afrilun 2023
daidai da 4 ga Shawwal, 1444.
Gidan
Kanawan Likoro an kafa shi ne shekaru fiye da 200 a garin Likoro dake karamar
hukumar Kudan ta jihar Kaduna ta yau. Malam Ibrahim, wani Dattijo mai shekaru 64
a duniya ya tabbatar da cewa; gidan ya samo asali ne a shekarar 1812 a lokacin
da ake karbar baki daga ko’ina da suka sauka a garin na Likoro; “bayan kamar shekaru
kamar 50 zuwa 60 da kafa gidan Kanawan Likoro aka yi zauren gidan Kanawa wanda
yanzu yake da shekaru 150”, a cewar Malam Ibrahim a yayin da yake gabatar da
tarihin gidan a lokacin taron.
Malam
Ibrahim ya ci gaba da cewa; “duk wanda ka ganshi a taron nan na yau ka dauke
shi a matsayin dan uwanka ne”. Ya kuma kara da cewa; a yanzu suna da mutane
daban-daban da suka fito daga gidan wanda ya ce; suna da Malamai, ‘yan kasuwa,
manoma da ma’aikatan gwamnati a matakai daban-daban. Ya nusasshe da cewa; gidan
ya zama sananne tun daga Legas har Maiduguri; “an san babban zauren gidan
Kanawa”, inji shi.
![]() |
Malam Ibrahim, Dattijo mai shekaru 64. |
Ya kuma labarta cewa; gidan na da sassa daban-daban wanda suka zama zuri’ar gidan wanda ya hada da sassan Alhaji Garba, Malam Yakubu Likoro, Nagoroji, Malam Sule da sauran su.
Sheikh Jamilu Saleh daya ne daga cikin zuri’ar gidan, a na shi jawabin ya karfafa ne akan muhimmancin sada zumunci. Inda ya kawo ayar Allah dake nuni da cewa; yankewa da kin sada zumunci barna ne a bayan kasa. Sannan ya kawo hadisin Manzon Allah (S) da yake cewa; duk mai son tsawon rai a duniya, to ya sada zumunci. “zumunci abu ne mai fadin gaske da girma”, ya kara nanatawa. Sannan ya karkare da karfafa su da yin hakuri da juna.
![]() |
Sheikh Jamilu Saleh |
Sannan
ya yi tilawar ayyukansu wanda ya ce ya hada da ziyarorin sada zumunci, ziyarar
asibitoti, daurin aure, ta’aziyyah, hada aure, sasanci, ayyukan jin kai da
sauran su. Shugaban ya ce; “tarihin Likoro ba zai cika ba sai an fado gidan
Kanawan Likoro”, inji shi.
Sai
dai ya ce daga cikin aikin da suka yi harda gyaran zauren gidan Kanawan Likoro
wanda ya shafe shekaru fiye da 150; “ba za mu zura ido zauren ya lalace a
zamaninmu ba shiyasa muka gyara shi”, ya tabbatar.
Shugaban
ya ce a nan gaba suna fatan a taro irin wannan su rika hada wa da daurin auren
zumunci a tsakanin ‘ya’yan gidauniyyar. “aure na daga cikin abin da ke hada
zumunci”, ya nusasshe.
![]() |
Dan Asabe Ibrahim, shugaban Gidauniyyar Gidan Kanawan Likoro yana gabatar a yayin taron. |
Ya
nemi da dukkanin ‘ya’yan gidauniyyar da su ci gaba da bai wa gidauniyyar gudummawa
domin ci gaban ayyukansu; “ilimi, kasuwanci, tarbiyyah, al’amuran da suka shafi
jama’a, samar da cibiyoyi na lafiya da na dogaro da kai na daga cikin kudurorin
kungiyarmu”, ya tabbatar.
A
yayin ganawarsa da manema labarai, ya yi karin haske da cewa; “mun samu
nasarori sosai, babban nasarar da muka samu akalla a zumuncin nan mun aurar da
mata da maza akalla guda biyar. A irin wannan taron wani ya ga wata, wata ta ga
wani, mun aurar, na daya ke nan. Na biyu; akwai wadanda aurensu ke tangarda mun
yi nasarar yanzu suna zaman lafiya. Akwai yaran da muka samo musu aikin yi.
Akwai wadanda muka samo musu gurbin karatu. Akwai wadanda ba su da lafiya mun
dauki nauyin rashin lafiyarsu”, ya tabbatar.
“burinmu shi ne mu ga wannan abin da na lissafa maka ya ci gaba. Misali; yaran nan da muka samo musu gurbin karatu idan sun kammala mu samo musu aikin yi. Akwai wadanda su kuma ba karatu bane a gabansu sana’o’i ne, mu ga cewa mun samo musu sana’ar yi”, ya lurantar.
Dan
Asabe Ibrahim, ya bayyanawa wakilinmu cewa sun gaji kungiyar ne daga wajen
iyayensu shekaru 10 da suka gabata. Kuma suna da shugabannin a kasashen
Saudiyya da Nijer, da ma dukkanin kananan hukumomin Nijeriya.
Kungiyar
a yayin taron ta karrama Alhaji Bello Abubakar Annur, shugaban kungiyar manoma
ta Nijeriya kuma daya daga ‘ya’yan kungiyar bisa Sarautar Danburam na Funtuwa da
ya samu.
![]() |
A yayin karramawar. |
A
yayin zantawarmu da Alhaji Sani Yushau, Mai Anguwan Anguwar Kanawan Likoro ya
ce abin da yasa suke karfafa batun auren zumunci a tsakaninsu shi ne “don kada
zumunci ya yi mana nisa, shiyasa muke karfafa wannan maganar aure”.
Alhaji
Sunusi, Sarkin Guibi, wanda ya fito daga garin Guibi ta karamar hukumar Kudan
ya ce, ya yi matukar jindadin halartar taron, inda ya yi kira ga dukkanin
wadanda suke gidan Kanawa, su so junansu da gaskiya; “ya zama abin ba a baki
kawai yake ba. Mu taimaki ‘yan’uwanmu da gaske. Mu duba ‘yan’uwanmu wadanda ba
su da abin yi a ba su abin yi domin wannan shi zai karfafa zumunci. Sannan sai
auratayya ta wannan yanayin zumuncin zai kara karfafa”, ya tabbatar.
Ya kuma karfafa kiransa akan shugabannin kungiyar da cewa; “kiran da nake yi ga shugabannin kungiya da su tsaya su natsu su yi nazari, su gane cewa matasan nan dalibai ne ko kuma wadanda ba sa karatu; idan wadanda suke karatu ne wacce hanya za a taimake su, idan kuma wadanda suka gama ne wacce hanya za a bi a taimake su a kan abin da ya shafi kasuwanci ko aikin gwamnati.”
![]() |
Alhaji Sunusi, Sarkin Guibi a yayin ganawa da 'yan jarida. |
Shima Alhaji Isiyaku Sadiq, Sarkin Zangon Shanun Zazzau, ya ce ya ji dadin wannan taron domin taron ya sake karfafa zumuncinsa da wasu. Sannan taron na bana ya fi tarukan baya armashi da bunkasa.
Shugabar
mata ta kungiyar, Malama Rukayyat Sa’id ta ce tana alfahari da kungiyar, kuma
daga cikin nasarar da ta samu a matsayinta na shugabar mata ta kungiyar shi ne
ta hada auratayya da kuma sasanta ma’aurata.
Ta
yi kira ga mata matasa na kungiyar da su dora daga inda suka tsaya ko bayan ba
su inda ta ce; “mu yanzu abin da muka yi tamkar dora gini ne, mun dora musu
ginin arziki muna son su dora bulo mai nauyi wanda yake sun wayi gari sun ga
muna yi, suma su dauki hannu su ci gaba. Wannan tafiya dari bisa dari mu dunga
tafiyar da shi har ko bayan ba mu. Suma ‘ya’yansu su taso su ga abin da suke
yi, jikokinsu su taso su ga abin da suke yi”, ta lurantar.
![]() |
Malama Rukayyat Sa’id |
Taron
na bana ya gudana ne a Kwalejin gwamnati ta Commercial dake Hayin Ojo a karamar
hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Wanda aka soma shi da misalin karfe 11 na
safe bayan budewa da addu’a da kuma karatun Alkur’ani mai girma daga Mulaikat
daga Kaduna sai kuma Aminu Sulaiman daga Kano.
No comments