Tababa da rashin tabbas yanzu haka sun mamaye Najeriya sakamakon rashin bayani daga hukumomin kasar akan shirin kidayar jama’ar da aka shi...
Tababa da rashin tabbas yanzu haka sun mamaye Najeriya sakamakon rashin bayani daga hukumomin kasar akan shirin kidayar jama’ar da aka shirya gudanarwa a makon gobe.
Bayanai sun ce Hukumar kidayar ta kasa ta shirya gudanar da aikin kidayar jama’a da kuma gidajen su ne daga ranar laraba mai zuwa wato 5 ga watan Mayu zuwa 7 ga wata, amma har ya zuwa wannan lokaci babu cikakken bayani ko shirin zai gudana.
Majiyoyi daga hukumar sun ce har ya zuwa yanzu ba’a kaiga horar da ma’aikata na wucin gadi da hukumar ta dauka ba domin gudanar da wannan aikin, yayin da hukumar ke kukan rashin isassun kudade.
Shugaban hukumar Nasir Isa Kwara ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a yammacin yau a fadar sa dake Abuja amma yaki cewa kowa uffan lokacin da manema labarai, cikin su harda wakilin RFI Hausa, suka tambaye shi dangane da aikin.
Ya zuwa yanzu dai babu tabbas ko aikin zai gudana a makon gobe ko kuma za’a sake dagewa har zuwa lokacin da sabuwar gwamnati zata kama aiki.
Najeriya ta dade tana kokarin kidaya jama’a domin tabbatar da sahihancin yawan al’ummar kasar amma a koda yaushe zai ta gamu da tuntube.
Tun a shekarar 2016 ake kokarin gudanar da wannan aiki amma har ya zuwa yanzu babu tabbas ko wannan gwamnati mai barin gao na iya kidaya jama’ar kasar kafin ta sauka daga karaga.
-Rahoton RFI Hausa
No comments