Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Zai Koma Gida Nijeriya Bayan Hutun Mako Biyar

  A Litinin din nan ne ake sa ran saukar zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a Abuja, babban birnin ƙasar. Zai koma Najeriya ne ba...

 


A Litinin din nan ne ake sa ran saukar zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a Abuja, babban birnin ƙasar.

Zai koma Najeriya ne bayan ya shafe tsawon mako biyar a Paris, inda ya huta, bayan kammala yaƙin neman zaɓen da ya ba shi nasara.

Tun farko an tsara cewa zaɓaɓɓen shugaban na Najeriya zai kwan biyu a Paris cikin ƙasar Faransa, daga nan kuma ya wuce zuwa birnin London, kafin ya dangana da ƙasar Saudiyya.

Sai dai rashin ganin sa a ƙasar Saudiyya lokacin aikin umra, musamman daidai lokacin da shugaban ƙasar mai barin gado, Muhammadu Buhari yake can, ya haifar da jita-jita da raɗe-raɗi.

Wani mataimakinsa na musamman Bayo Onanuga ne ya tabbatar da rahoton komawar Tinubun Najeriya, ko da yake bai cewa ga taƙamaimai lokacin da zai sauka a ƙasar ba.

No comments