*Ba kuma sai ranar Kudus kadai ake nuna damuwa da ta’asar da ake yi ma Falastinu ba Daga Ammar M. Rajab Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya,...
*Ba kuma sai ranar Kudus kadai ake nuna damuwa da ta’asar da ake yi ma Falastinu ba
Daga Ammar M. Rajab
Jagoran Harkar
Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa wajibi ne nuna
damuwa da al’amarin al’ummar kasar Falastinu. Shehin Malamin ya bayyana hakan
ne a ranar Laraba 12 ga watan Afrilun 2023 daidai da 21 ga watan Ramadan 1444 a
wani faifan bidiyo da aka saki a gidansa dake birnin Tarayya Abuja.
Shehin Malamin ya soma
jawabinsa ne da tunatar da al’umma cewa ranar rana ce da ta dace da Shahadar Sayyidina Ali Bn Abi Dalib, wanda ya
ce; “Shahadar Amirulmuminin (AS) ne. Wanda aka sara ranar 19 ga watan Ramadan,
ruhinsa tsarkakka ya bar gangan jikinsa a yammacin 21 ga watan Ramadan. Saboda
haka muna taya al’umma jaje”.
Daga nan ne Shehin
Malamin ya ci gaba da cewa; “kuma a gabanmu, jibi (gobe) Juma’a akwai ranar
Quds na duniya, wanda akan nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu kan ta’asar da
ake musu a mamayar da aka musu. To kuma na bana, ya zama ya fita daban da na
sauran shekaru. Saboda tun kamawar Rajab, mutanen nan (Isra’iliyawa) sai sun yi
kisan kai. Kullum sai an kashe Bafalasdine. Wannan al’amari yana da
ban-al’ajabi. Kuma da Ramadan ya kama sai aka shiga tsanantawa, yanzu Masjidul
Aqsa ne za su je su tarwatsa masu sallah, ba su damu ba su kakkama mutane su
daddaure. Hotuna na iya nunawa idan mutane sun damu da su gani” ya lurantar.
Ya ci ga ba da cewa; “To,
a bara mun karfafa guiwar mutane a kan nuna ‘Tadamuni’ da al’ummar Falasdinu.
Akwai wani abu da ake yayin cewa a rika daga tutar Palasdinu, suna cewa;
#FlyThePalastenianFlag. To kuma Alhamudulillahi, ‘yan’uwa a muzaharorinsu a nan
Abuja duk su kan rika daga tutar Falasdinu ko da ma muzaharar suna yi a kan
wani abu ne, ranekun Litinin da ranar Juma’a da wasu raneku da su kan yi
Muzaharori, duk suna rika daga tutoci. Saboda haka yana da kyau a daidai wannan
lokaci a rika daga wadannan tutoci na nuna cewa muna tare da al’ummar Palasdinu”,
ya karfafa.
Shaikh Ibraheem Zakzaky
ya ce; nuna ana tare da al’ummar Falasdinu abu ne da ya dame mu duk cikarmu, inda
yake cewa; “Domin Falasdinawan nan da ake ta faman kashewa, a madadinmu suke
wannan gwagwarmaya, - a madadin dukkan al’ummar Musulmi ne. Domin kuwa wadanda
suke musu abin da suke musu, idan suna iyawa, to za su yi ma kowa da kowa. Kuma
ba su ma boye ba, akwai wani makiyin Allah makiyin Annabi (S), wanda yake cewa
wai yakin duniya na uku, duk wanda ma bai ce yana nan tafe ba, kamar bai san
abin da yake yi bane. Wai yana nan tafe. Kuma a lokacin ya ce, za su kona
Musulmi. Za su kona Larabawa. Bai ko boye ba. Ya ce, za su kona su ne kurmus.
Haka ya ce”.
“Kila za ku san shi,
baro-baro yake wannan maganar. Saboda haka su abin da suke tunani shi ne, su za
su yi fada ne da al’ummar Musulmi gaba daya. Kuma hankoronsu ba Falasdinu ne
kawai ba, za su kafa daular Isra’ila ce da za ta mamaye dukkanin wannan
yankunan, wanda ya hada kasashen Falasdinu, da Urdu, da Siriya da Arewacin
kasar da ake ce ma Saudi Arebiyya, har da Birnin Madina. Su a wajensu wai suna
cewa wai Birnin Madina ma wai birninsu ne, wai da Yahudawa ne a wajen kafin wai
Annabi (S) ya je ya kore su. Ko da yake ba Annabi suke ce masa ba. Wai ya je ya
kore su. Kamar yadda suke cewa wai ya karkashe su ya kore su a kasar, wai
kasarsu ce. Saboda haka sun zana taswira wanda suka saka Madina a ciki, su a
wajensu za su mamaye wannan wajen ne, kuma tunaninsu ke nan. Insha Allahu
wannan mafarki na su ba zai taba yiwuwa ba. Amma kuma dai mafarki ne kuma suna
ta ta’asarsu”, ya lurantar.
Shehin Malamin ya ci
gaba da cewa; “Saboda haka, ya kamata duk al’ummar Musulmi su nuna damuwarsu. A
yi shirin wannan Ranar Quds, a yi ta a ko ina. Mun san cewa da mun zabi wadansu
birane ne musamman muka ce a nan ne za a yi Quds, da kamar birni 22 muke yi, to
amma saboda irin yanayin tsaro da aka jefa kasar nan a ciki, wanda
tafiye-tafiye ma da wahala, saboda haka sai ya zama wadansu birane ma da ba a
saba yi ba duk an yi bara, bana ma haka nan. Saboda haka za a iya yi a biranen
da ma ba a saba yi ba. In zai yiwu, yana da kyau a je a yi a manyan birane, in
ma ba zai yiwu ba, wadansu biranen da ba a saba yi ba ma du kana iya yi. Ba
kamar Ashura da muka ce ko a kauyuka za a iya yi ba, ita ranar Quds ranar
‘Tadamun’ ne, kamata ya yi ita duniyar ta gani muna tare da su, (don haka) za a
yi a muhimman wurare”, ya jaddada.
Shehin Malamin ya
karkare da cewa; “Ba kuma kawai ranar Quds ne za mu nuna ‘Tadamuni’ da al’ummar
Falasdinu ba, duk wannan lokacin da ake musu wannan ta’asar ya kamata mu nuna,
tunda sauran duniya ma suna yi. Idan mutum yana bibiyan labaru zai ga a sauran
biranen duniya, duk an ta fitowa ana nuna rashin goyon baya ga irin ta’asar da
ake ma al’ummar Falasdinu a wannan wata mai tsarki na Ramadan. Saboda haka bai
kaman a ce mu sai ranar Quds din ne kawai za mu yi ba, a kowane lokaci ma ya
kamata ya zama muna nuna ‘tadamun’, a zantukanmu da kalamanmu da
rubuce-rubucenmu a jaridu, da kuma shafuffuka na yanzu (da ake) zamanin
‘internet’, da kuma wakoki da ire-irensu, duk a rika tunatar da al’umma, a
fadakar da ita kan abin da ke faruwa a al’ummar Palasdinu, ya zama ya shafe mu
gaba dayanmu”, ya shawarci al’umma.
No comments