Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Wani Ma Sana'ar POS Ya Kashe Miliyan 280 Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure

  Jami'an tsaron 'yan sanda a Najeriya sun kama wani dan PoS Alfa Rafiu bisa zarginsa da kashe da Naira miliyan 280 da aka tura asus...

 


Jami'an tsaron 'yan sanda a Najeriya sun kama wani dan PoS Alfa Rafiu bisa zarginsa da kashe da Naira miliyan 280 da aka tura asusun bankinsa bisa kuskure. 

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ce wanda ake zargin,  mazaunin unguwar Akuji ne da ke a karamar hukumar Ilorin ta yamma. 

A cewar majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin,suka ce ba zato ba tsammani aka ga Rafiu na wadaka da kudi a makonnin da suka gabata. 

“Kusan makonni biyu da suka gabata, kudaden wadanda suka kai miliyan N280mn, yana jin saukarsu maimakon ya jawo hankalin bankinsa kan abin da ke faruwa, kawai sai ya buge da almubazaranci da su ya sayi wannan ya sayi wancan. 

“Rafiu ya sayi gidaje da motoci, sannan ya dauki nauyin tura mutane da dama zuwa aikin Umarah. Wasu daga cikin wadanda ya tura a yanzu haka da muke magana da kai suna Saudiyya ba su dawo ba. 

Majiyar ta kara da cewa "Duk da cewa ya samu kyakkyawar shaidar zama mutumin kirki wurin al’umma, amma da dama sun yi mamakin kudancewarsa cikin kankanin lokaci a matsayinsa na dan PoS." in ji majiyar 

Rundinar ‘yan sandan jihar sun tabbatar da kama Alfa Rafiu, amma suka ce yana hannun hedikwatar Sashen Binciken Manyan Laifuka (FCIID) da ke Lagos.  

-Rfi Hausa

No comments