Marigayi Shamakin Gwantu Daga Muhammad A. Dalhatu Wazirin Gwantu III, Malam Waziri Isa Adam Aliyu, ya yi rashin babban yayansa, Shamakin G...
![]() |
Marigayi Shamakin Gwantu |
Daga Muhammad A. Dalhatu
Wazirin Gwantu III,
Malam Waziri Isa Adam Aliyu, ya yi rashin babban yayansa, Shamakin Gwantu, Malam
Muhammadu Waziri Adam Aliyu.
Jaridar MADOGARA ta
samu labarin cewa; marigayin ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Alhamis, bayan
ya yi rashin babban dansa, Malam Jibrin Muhammad Waziri Adam wanda shima ya
rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Shamakin Gwantu mai
shekaru 69, tuni aka bizne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin
Gwantu. Ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya takwas da kuma jikoki 20.
Dan Marigayi Shamaki,
Malam Jibrin, wanda shi ne wanda ya jima yana kula da mahaifin a lokacin da
yake jinya tun farkon wannan shekarar, ya kasance cikin koshin lafiya a
makonnin da suka gabata, sai dai cikin kankanin lokaci ya yi rashin lafiya kuma
ya rasu kwanaki hudu kafin mahaifinsa.
![]() |
Marigayi Malam Jibrin Muhammad |
No comments