Daga Muhammad A. Dalhatu Jaridar MADOGARA a ranar 6 ga watan Maris ta samu takardar gayyata daga Gidauniyyar ‘Zahra Relief Foundation’ domin...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Jaridar MADOGARA a ranar 6 ga watan Maris ta samu takardar gayyata daga Gidauniyyar ‘Zahra Relief Foundation’ domin halartar aikin ciyarwar abincin buda baki ga mabukata a cikin watan Ramadan a birnin Tarayya Abuja.
A cikin takardar gayyatar wanda Abdurrahman Muhammad ya sanyawa hannu a madadin gidauniyyar ya bayyana cewa; “ita dai Zahra Relief Foundation gidauniyya ce da take ayyukan jinkai da tallafi ga mabukatan Harka Islamiyya da al’umma baki daya kamar marayu, ‘yan gudun hijira, miskinai, da mabukata ko wadanda ibtila’i ya afma ma da sauran su”.
“za a yi ne a Abuja da sauran wasu jihohin kasar a cikin watan Ramadan a gidajen marayu, sansanin ‘yan gudun hijira, da wuraren zaman al’umma”, sanarwar ta tabbatar.
Wakilinmu a birnin Tarayya Abuja, ya shaida wannan rabon na ciyar da al’umma mabukata a cikin watan Ramadan mai alfarma da ta gabata.
A ranar 10 ga watan Afrilun, wakilinmu ya shaida mana cewa an yi rabon abincin buda bakin ne a Area 1 dake babban birnin Tarayya Abuja, a inda al’umma da dama ne suka amfana da wannan tallafi na abinci. A yayin ganawa da wadanda suka amfana da wannan tallafin sun nuna farin cikinsu da godiyarsu inda daya daga cikinsu mai suna Muhammad Salisu ke cewa; “da za a rika samun al’umma a daidaiku da kungiyance suna bayar da irin wannan tallafi a irin wannan lokaci da bayan Ramadan ma da al’umma sun samu saukin rayuwa da rage fargabar abin da za a ci a yayin buda baki”.
Kazalika washegarin wannan rana, tawagar masu rabon abincin sun dira a Anguwar Life Camp dake Abuja inda suka yi wannan rabon abincin.
A ranar 12 ga watan Afrilun 2023, tawagar rabon kayan abincin ga mabukata ta zagaya Anguwannin mabambanta a cikin birnin Tarayya Abuja domin bai wa mabukatan abincin da za su samu su yi buda baki.
Har wala yau a ranar 13 ga Afrilu ne, gidauniyyar ta isa masallacin kasa dake birnin Tarayya Abuja, a inda a nan ma ta raba kayan abincin ga mabukata musamman wadanda suka halarci masallacin.
Tawagar a yayin ganawa da daya daga cikinsu, ya shaida mana cewa; “an raba abincin ne ga al’ummar Musulmi mazauna wurare daban-daban domin hidimtawa da kuma saukakawa ga mutane a watan mai alfarma”, ya tabbatar.
A ranar 15 ga Afrilu kuwa, tawagar ta shiga Anguwannin Jabi ne da Kado duk a cikin Abuja domin su ma mabukatan yankin su amfana daga hidimar gidauniyyar.
Haka gidauniyar ta rika zagayawa Anguwanni daban-daban har zuwa karshen watan Ramadan tana raba abincin ga mabukata kamar yadda wakilinmu ya labarta mana.
Ita dai gidauniyyar Zahra Relief Foundation an kafa ta ne a shekarar 2011 , inda tun daga lokacin ta fara ayyukan ciyarwa da hidimtawa al’umma da ayyukan jin kai.
Gidauniyya ce dake karkashin Harkar Musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a a karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky
No comments