A Nijeriya, cacar-baki ta kaure tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da na jam'iyyar Labour mai adawa. Lamarin na...
A Nijeriya, cacar-baki ta kaure tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da na jam'iyyar Labour mai adawa.
Lamarin na zuwa ne, tun bayan jin wata tattaunawar wayar salula tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi da Bishop David Oyedepo, wani babban limamin Kirista na majami'ar Living Faith Church.
A ƙarshen mako ne, wata jaridar intanet mai suna People Gazette ta wallafa wannan murya da aka kwarmata, tsakanin Peter Obi da babban limamin Kiristan, Bishop David Oyedepo.
Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a ƙasar.
Musamman ma yadda aka ji ɗan takarar yana roƙon malamin ya taimaka wajen nema masa goyon bayan mabiya addinin kirista da ke shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da kuma shiyyar arewa ta tsakiyar ƙasar.
Ya dai alaƙanta siyasar da takararsa, tamkar wata fafutukar yaƙi na addini, har ma ya tattabar wa limamin Kiristan da cewa ba za su yi da-na-sanin goya masa baya ba.
`Yan jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya sun yi ca a kan dan takarar shugaban kasar suna cewa asirin sa ne ya tonu, kuma zargin da suke yi cewa siyasar sa ta addini da kabilanci ce ya tabbata.
A hirarsa da BBC, Mallam Ali M Ali, daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu, ya ce 'yar manuniya ta nuna kan zargin da suka yi tun da farko na salon yadda ɗan takarar ta LP ke amfani da addini a gangamin yaƙin neman zaɓe.
''Kurunkus, siyasar Peter Obi da jam'iyyar Labor ta zo ƙarshe, sai dai a je, a yi jana'izarta wataƙila hakan zai zama izna ga masu amfani da bambancin addini domin raba kan al'umma."
Ya ƙara da cewa: " Ta tabbata salon yaƙin neman zaɓensa, na da nasaba da raba kawunan jama'a ta hanyar amfani da addini, don neman mulki.''
Tuni dai kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Mista Kenneth Okonko ta tabbatar da gaskiyar tattaunawar, amma ya ce an yi mata mummunar fahimta.
Sai dai kuma tun ba a je ko'ina ba, Dr Yunusa Tanko, wanda shi ma ke magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen Mista Obin ya ce sautin tattaunawar da jaridar People Gazette ɗin ta fitar, yarfe ne kawai, saboda a iya saninsu ba a yi wannan tattaunawar ba.
Shi ma Bishop Oyedepo a wani martani da ya mayar, bai ce ya yi tattaunawar nan da Msita Peter Obi ba.
![]() | ||
Bishop David Oyedepo da Peter Obi |
Martanin Oyedepo
Shugaban cocin Living Faith Worldwide, Bishop Oyedepo ya ce bai taba yi wa wani dan siyasa kamfe ba, ko kuma kokarin shawo kan wasu al’umma su zabi wani ba.
Ya fadi hakan ne a lokacin da yake yin huduba a cocin tasa da ke da cibiya a yankin Ota na jihar Ogun a ranar Lahadi.
Ya ce “Ban taÉ“a yi wa wani kamfe ba ko kuma yi ma wasu magana a madadin wani ba, kuma ba zan taÉ“a yi ba har na mutu.”
Sai dai babban limamin Kiristan bai ambato batun muryarsa da aka ji a hira da É—an takarar shugaban Æ™asa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ba.
Mene ne abin da Peter Obi ya ce?
A cikin muryar da aka naÉ—a ta wayar tarho da Peter Obi ya yi da Bishop Oyedepo, wadda BBC ba ta tantance gaskiyar ta ba, an ji Obi yana cewa “Daddy, ina son ka yi wa mutanenka na Kudu-maso-yamma da Kwara magana, Kiristoci na Kudu-maso-yamma da Kwara.”
Ya Æ™ara da cewa “Wannan yaÆ™i ne na addini.” Inda shi kuma Bishop Oyedepo ya amsa da cewa “Na yarda da hakan, na yarda da hakan, na yarda da hakan.”
Obi ya ci gaba da cewa “Kamar yadda na sha faÉ—i – idan komai ya tafi daidai, ba za ku yi da-na-sanin goya min baya ba.”
Sai Oyedepo ya ce “Muna nan muna kallon abin da Allah zai yi.”
No comments