Daga Idris Umar Zariya Mukaddashin Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa, FRSC, Dauda Ali Biu, ya bayyana yadda jami'an H...
Daga Idris Umar Zariya
Mukaddashin Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa, FRSC, Dauda Ali Biu, ya bayyana yadda jami'an Hukumar suka taimaka wajen takaita hadurra a yayin bukukuwan sallah karama.
Kwamandan ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da 'yan jarida a yayin bikin Hawan Daushe da ya gudana a Masarautar Zazzau ta jihar Kaduna.
Dauda Biu ya fara ne da bayyana dalilinsa na halartar bikin, inda ya ce; "muna nan ne domin halartar bikin sallah. Mu kuma taya al'ummar masarautar Zazzau murna tare da Sarki da kuma gwamnan jihar Kaduna. Wannan shi ne makasudin kasancewarmu a nan da wannan safiyar", ya jaddada.
Da yake bayyana yadda bikin sallar na bana ta kasance, ya bayyana cewa; bukukuwan sallar na bana ya kasance cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Inda ya ce babu wani rahoton tashin hankali suka samu. Inda ya ci gaba da cewa; "a bangarenmu mun taimaka wajen walwalar ababen hawa. Sannan mun takaita hadura. Wannan shi ne abin da muka yi lokutan bukukuwan murnar sallah. Za mu Kuma ci gaba da hakan har lokutan bayan sallah", ya tabbatar.
Ya kuma kara da cewa; "saboda yanzu akwai tafiye-tafiye da yawa, mutane za su tafi murnar bukukuwan sallah kuma bayan haka za su dawo muhallansu. A don haka muna kan ayyukan koyaushe akan tituna".
Da yake bayyana yadda ya ga hanyar, Daua Ali Biu ya ce; "na yi tafiya daga Abuja zuwa Zariya ta titi. Mun yi tunanin cunkoson ababen hawa. Amma cikin ikon Allah muka raba jami'anmu musamman a titin Kaduna zuwa Abuja, mun yi kokarin ganin mun tabbatar da walwalar ababen hawa. Babu labarin wani matsala".
A karshe ya jinjinawa jami'an Hukumar ta FRSC, da kuma sauran jami'an hukumomin tsaro bisa gudummawar da suka vayar a yayin bikin sallar, inda ya ce; "zan yi amfani da wannan dama wajen jinjinawa tare da yabawa jami'anmu na hukumar kiyaye hadurra ta kasa da sauran jami'an tsaro bisa wannan kyakkyawan aiki da suka gudanar", ya karkare.
No comments