Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda ‘Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Kusan Mutane 80 A Zamfara

  A karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya sama da mutane 80 ne 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su...

 


A karamar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya sama da mutane 80 ne 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a jiya Juma'a.

Mutanen da lamarin ya ritsa da su kamar dai yada rahotanni suka tabbatar daga yankin, bayan isar su daji wajen neman ita ce da safiyar Juma’a, sai labarin sace wasu daga cikin mutanen yankin daga 'yan bindiga ya kuno kai, a daidai lokacin da wasu ke cikin aiki a gonakinsu.

Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara mai suna Sani Wanzamai ya ce an yi garkuwa da yara kusan 80 daga kauyen Wanzamai tare da wasu fiye da 20 daga kauyen Kucheri da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar da kuma al’ummar Yankara a makwabciyar Katsina.

Ana sa ran yawan mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su tsakanin 80 zuwa 100, yawancinsu matasa ne tsakanin shekarun 15-18 da wadanda suka kai shekaru ashirin. Akwai wani Dattijo wanda shekarunsa hamsin ne. Sai dai yawancin wadanda aka yi awon gaba da su matasa maza da mata ne.

Ya zuwa wannan lokaci ana dakon sanarwa daga rundunar tsaro domin tabbatar da aukuwar wannan al’amari.

No comments