Gidan Rediyon Faransa, wato RFI Hausa ya labarto cewa; iyayen daliban Nijeriya da suka makale a Sudan sun bayyana aniyarsu ta nemawa ‘ya’y...
Gidan Rediyon Faransa, wato RFI Hausa ya labarto cewa; iyayen daliban Nijeriya da suka makale a Sudan sun bayyana aniyarsu ta nemawa ‘ya’yansu mafita domin su samu damar ficewa daga kasar, da a halin yanzu rikici ya daidaita.
Tun a makon da ya gabata ne dai gwamnatin Nijeriya ta shirya kwashe daliban zuwa kasar Masar dake makwabtaka da Sudan din, don samun sauki wajen dawowa gida, toh sai dai bayanai na nuna hukumomin Masar sun ki amincewa ‘yan Nijeriyar su shiga kasarsu.
Ya zuwa yanzu ‘ya’yan Nijeriyar da suka kaura daga babban birnin Khartum na Sudan tun a ranar Laraba da ta gabata don isa Cairo kamar yadda hukumomin kasar suka tsara tun farko, na ci gaba da kasancewa a makale a kan iyakar kasashen biyu.
Iyalan ‘yan Nijeriyar da ke ci gaba da kasancewa a Sudan sun shaidawa jaridar Daily Trust a daren ranar Asabar cewa babu hikima a tsarin bin hanya guda wajen dawo da ‘yan kasar gida.
No comments