Daga Muhammad Farouk 'Yan bindiga sun bindige mata biyu har lahira a yayin da suka tare hanyar Katuru mai nisan kilomita 2 zuwa kwaryar ...
Daga Muhammad Farouk
'Yan bindiga sun bindige mata biyu har lahira a yayin da suka tare hanyar Katuru mai nisan kilomita 2 zuwa kwaryar garin karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara a yau Lahadi.
Majiyoyi daga yankin sun shaida wa RFI Hausa cewa har ya zuwa lokacin da ake wannan zance, gawarwakin matan da aka kashe na kwance a hanyar ba a dauke su ba.
Har ila yau a cikin garin Shinkafin, ‘yan bindiga sun kashe wasu ‘yan kasuwa, Jamilu Jarma da wani wanda ake kira Oke, suka kuma yi awon gaba da dukiyarsu a ranar Asabar zuwa wayewar garin Lahadi.
Mazauna garin Shinkafi sun koka a kan yadda ‘yan bindiga suka addabe su a ‘yan kwanakin nan, inda suke kai musu hare-hare ba kakkautawa tun bayan da aka kammala zabukan Nijeriya.
No comments