Daga Muhammad Farouk Hadaddiyar Daular Larabawa ta United Arab Emirates (UAE) ta nemi al'ummar Musulmin kasar da su fara ...
Daga Muhammad Farouk
Hadaddiyar Daular Larabawa ta United Arab Emirates (UAE) ta nemi al'ummar Musulmin kasar da su fara duban watan Shawwal a jibi Alhamis.
Hukumomin daular ta ce duk da masana falaki sun tabbatar da cewa zai yi wuya a ga watan da ido ko kuma da na'ura a wannan rana, amma dai ya zama wajibi a duba watan a ranar Alhamis kamar yadda Jaridar Khaleej Times ta labarto.
Sai dai rahoton ya fayyace cewa za a iya ganin watan a ranar Alhamis musamman a Afrika ta Yamma da Afrika ta Arewa idan aka haska da na'ura a wadannan yankuna amma ba za a iya ganinsa da ido ba.
No comments