Wani sabon ɗan Majalisar Wakilan Najeriya da aka zaɓa daga jihar Taraba ya rasu ranar Juma'a 21 ga watan Afirilu, makonni ƙalilan kafi...
Wani sabon ɗan Majalisar Wakilan Najeriya da aka zaɓa daga jihar Taraba ya rasu ranar Juma'a 21 ga watan Afirilu, makonni ƙalilan kafin a rantsar da su.
Ismaila Maihanci wanda aka zaɓa don wakiltar mazaɓar Jalingo da Yorro da Zing a Majalisar Wakilai ya rasu ne bayan wata gajeriyar jinya a Abuja.
Wani makusancin zaɓaɓɓen ɗan majalisar ne ya tabbatar wa BBC bayanin rasuwar inda ya ce mutuwar ta ɗimauta iyalansa da kuma makusanta.
Ya ƙara da cewa wannan babban rashi ne ga al'ummar jihar Taraba gaba ɗaya.
Ba don rasuwar tasa ba, zai kasance karon farko kenan da Isma'ila Maihanci, ɗan jam'iyyar PDP, zai je majalisar tarayya bayan ya kayar da mutumin da ke kan kujerar, Kasimu Bello Maigari na APC.
Ismaila wanda ya samu nasara a zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu ya kasance ɗaya daga cikin fitattun matasan 'yan siyasa a jihar Taraba.
An haifi marigayi Isma'ila Maihanci ne cikin watan Oktoban 1986. Kuma ya rasu ranar Juma'a 22 ga watan Afrilu yana da shekara 37.
Marigayin ya yi fice ne kasancewarsa ɗan kasuwa kuma matashin ɗan siyasa a jihar.
An tsara za a yi jana'izar Hon Isma'ila Maihanci ne a fadar Sarkin Muri, Mai martaba Alhaji Abbas Jidda Tafida.
A cewar wani abokin marigayin kuma mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓensa, Kwamrade Sani Bamalo (AKA Mai tarko na Kwamanda), za a ɗauki gawar marigayin daga Abuja zuwa Yola a ranar Asabar.
"Daga Yola, ambulance zai ɗauko shi zuwa Jalingo".
Sai dai rashin kyawun hanya in ji Kwamared Bamalo, ya sa jana'izar ba za ta yiwu ba a ranar, don haka sai aka bari kawai sai washe gari Lahadi.
'Mutuwarsa ta zo da mamaki kamar cin zaɓensa'
Ya ce sun yi rububin yaƙin neman zaɓe na ɗan majalisar wakilai, har ya ci zaɓensa lafiya.
A lokacin zaɓen gwamna da 'yan majalisun dokoki na jihohi ne, cewar Kwamared Bamalo, Isma'ila ya fara jinyar da ake tunanin ita ce ta zama ajalinsa ranar Salla.
A cewarsa, marigayin bai jima yana jinya ba.
"Lafiyarsa ƙalau, muka yi gaishe-gaishe bayan ya ci zaɓe. Da aka fara ba da shaidar cin zaɓe, ya je Yola ya hau jirgi zuwa Abuja, inda ya karɓi takardarsa".
Ya ce Hon Isma'ila Maihanci ya lashe zaɓe ne bayan kaɗa ƙuri'a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Sani Bamalo ya ce a tarihi, marigayin ne ɗan siyasa na farko, da ya ci zaɓe a jam'iyya mai mulki a cikin garin Jalingo, wanda babbar tungar 'yan adawa ne.
"An yi al'ajabi a zaɓensa, haka kuma mutuwarsa ya zaman mana abin al'ajabi," ya ƙara da cewa.
Hon Isma'ila Maihanci ya taɓa riƙe muƙamin sakataren jam'iyyar PDP a mazaɓar Sintali da ke cikin garin Jalingo, in ji Sani Bamalo.
Kuma ya kasance mai ba da shawara na musamman ga gwamnan Taraba har karo biyu kafin ya ci zaɓen fidda gwani.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen marigayin ya ce Maihanci ya rasu ya bar matar aure ɗaya da ɗa ɗaya.
No comments