Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zababben Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Ya Bayyana Kwamiti Mai Mutum 60 Na Karbar Mulki

  Daga Muhammad A. Abubakar Zababben gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa kwamiti mai mutane 60 a yayin da yake shirin karbar mulki. ...

 


Daga Muhammad A. Abubakar

Zababben gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa kwamiti mai mutane 60 a yayin da yake shirin karbar mulki. 

Ofishin zababben gwamnan ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris ya sanyawa hannu a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa kwamitin yana da alhakin tuntubar gwamnatin Gwamna Bello Matawalle mai barin gado, gabanin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu a jihar. 

Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, MD Abubakar CFR ne zai jagoranci kwamitin, a yayin da Dr. Hamza Mohammed zai zama Sakatare.

Har ila yau, kwamitin ya hada da tsohon shugaban ma'aikata na jihar Zamfara, Mujitaba Isah Gusau; Kanal Bala Mande (mai ritaya); Farfesa Abubakar Aliyu Liman; Barista Nura Ibrahim Zarumi; Barista Bello Galadi, da sauransu.

Kwamitin dai ya kunshi masu fasaha, masu rike da mukaman gwamnati da masu ritaya da kuma kwararru da masana daga kowane bangare na rayuwa.

Babban aikin kwamitin shi ne samar da tsarin tuntuɓar juna tare da kafa hanyar sadarwa ta yau da kullum tare da gwamnati mai barin gado domin karbar mulki cikin sauƙi.

Bugu da kari, kwamitin zai tuntubi ma’aikatu, sassa da hukumomi (MDAs) tare da duba kudaden gwamnati mai barin gado tare da mai da hankali kan rasit, kadarori, da lamuni da sauransu.

Nan gaba kadan ne za a bayyana ranar da za a kaddamar da kwamitin karbar mulkin na Gwamna.


No comments