Daga Sulaiman Bala Idris Fassarar Muhammad A. Abubakar A wata hira da sashen Hausa na DW, gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Bello Moha...
Daga Sulaiman Bala Idris
Fassarar Muhammad A. Abubakar
A wata hira da sashen
Hausa na DW, gwamnan jihar Zamfara mai barin gado, Bello Mohammed Matawalle, ya
yi wani ikirari kan dalilan da ya sa ya sha kaye a zaben da ya gabata. Sannan
ya yi zargin cewa an yi amfani da karfin soja domin dakile damarsa.
Shan kayen da Matawalle
ya yi shi ne babban kaduwa a babban zaben 2023. Ya sha kaye ne a hannun wani
tsohon ma’aikacin banki da bangaren jam’iyyar APC ke yi masa ba’a a matsayin
dan siyasar da bai da gogewar da ake da bukata domin lashe zaben karamar hukuma.
Sai dai a wani yanayi na daban, a hukumance an bayyana wannan dan siyasar da ba
shi da kwarewa a matsayin zababben gwamnan jihar.
Abin da ya faru a
Zamfara wani gangamin taron dangi ne da wasu wanda suka hada da shugaba mai ci,
da tsoffin gwamnoni uku, da duk wasu manyan ‘yan siyasa da suka hada kai suka
fafata da wani sabon dan siyasa da ya shiga harkar siyasar a shekarar 2018.
Hakika wannan sauyi ne na siyasar karni da aka rubuta shi da babbar tawada a
tarihin siyasar jihar Zamfara.
Matawalle da jam’iyyar
APC sun yi amfani da duk wata dama domin yin magudin zabe, tun daga kan kokarin
kawo cikas ga zaben zuwa sace tattara sakamakon zabe daga rumfunan zabe, Unguwanni,
da kuma kananan hukumomi.
Wannan dai shi ne
Matawallen da ake zargin da ya sace jami’in hukumar zabe ta INEC na garinsu,
wato karamar hukumar Maradun, domin sake rubuta sakamakon zabe tare da ware wa
kansa kuri’u na bogi da ba za su misaltu ba—godiya ga shafin IREV dake tattara
sakamakon zabe bisa wannan ceto.
Yana da matukar wahala
a yarda cewa babban mai bayar da tsaro na jihar da ‘yan bindiga suka addaba ne zai
fito a fili ya yi ikirarin cewa an girke sojoji 50 a kowace rumfar zabe a fadin
jihar. Wannan magana ta isa dalilin da yasa mutanen Zamfara suka ki Matawalle.
Ya yi nuni da cewa bai san tsarin tsaro na kasar nan ba, gami da jimillar
ma’aikatan da ke aiki a kowanne sashen tsaro.
Jihar Zamfara na da
jimillar rumfunan zabe 3,529. Ban san wanda ya koyar da gwamna ilimin lissafi
ba, amma dole ne ya zama malami mai ban tsoro. Idan kun ninka 50 sau 3,529,
zaku sami 176,450.
Misalin Gwamna
Matawalle shi ne sojoji 176,450 aka tura Zamfara. Mu fada masa gaskiya ne ko
kuma mu bar shi gaskiyar ta tashe shi daga barci? Mafi kyawun zaɓin da ya rage
masa shi ne ya mutunta zabin mutane tare da yin ritaya cikin shiru domin ya
ceci kansa daga ƙarin kunya.
Rundunar sojin Nijeriya
na da sojoji kusan 230,000, amma Gwamna Matawalle na son ya nuna cewar sojoji
53,550 ne kawai aka tura su wasu jihohin Nijeriya a ranar zaben gwamna; sauran sojoji
176, 450 an tura su ne Zamfara.
A wannan lokaci, yana
da wahala ga duk mai hankali ya fahimci me Matawalle ke ƙoƙarin tabbatarwa da
maganarsa domin ya saba wa hange da hankali. Ko da yake, ya saba dama, a lokuta
da daban-daban, yana tabbatar da sakacinsa a ayyukansa har ma da kalamansa. Za
mu iya kau da kai da wasu kalamai na gwamnan wanda ya yi amannar cewa sauya
sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki ne kadai zai sabunta masa nasarar takararsa
ta biyu. Dole ne har yanzu yana cikin tsananin kaduwa. Amma maganganun rashin
hankali da ka iya karkatar da gaskiya sune abin da ba za a taɓa yarda da su ba.
Hukuncin ikirarin
Gwamna Matawalle KARYA ce. Ba dalibin firamaren da zai fahimci wannan iƙirari
na ban dariya. Gwamnan ya bayyana ne domin kawai ya samu masu tausaya masa. Yana
kokarin ya sauya labarin cewa mutane ne suka yi watsi da shi kuma suka ki shi,
suka kada shi.
Al’ummar Zamfara masu
juriya sune wadanda suka toshe duk wata hanya domin yin magudi, sannan bai
kasance kasuwanci ba kamar yadda aka saba. Tabbas matasan jihar Zamfara da suka
gaji da salon mulkin Matawalle ne suka haddasa faduwarsa. ‘Yan fansho da aka
cire musu kudadensu daga tsarin fansho wanda ba a san inda aka sa ba suna daga
cikin wadanda suka kayar da shi.
Duk baya ga haka nan, abin
da ya faru da Matawalle daga Allah ne. Kada ya manta, an dauke shi a wani
faifan bidiyo yana cewa: “Idan har na taba cin amanar PDP, kada Allah yasa na
zauna lafiya har zuwa karshen rayuwata, na rantse da Allah. Idan har zan iya
barin PDP ko kuma na yaudari daya daga cikin membobinmu, Allah ya hukunta ni.”
Maganar ta isa haka
nan, mai girma gwamna. Yanzu lokaci ne da za ka duba baya ka kuma tuba. Farin wata
sabuwa ce ta bayyana ga jihar Zamfara.
Bala ya rubuto ne daga Gusau ta jihar Zamfara.
No comments