Daga Sulaiman Bala Idris “Kun yi failing, ku zo ku kwashe kayanku…” Kuskure na farko da jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi shi ne, d...
Daga Sulaiman Bala Idris
“Kun yi failing, ku zo ku kwashe
kayanku…”
Kuskure na farko da jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi shi ne,
daukar wakar da ke sama da wasa, wanda za a iya fassarata da cewa ‘Kun fadi, ku
zo ku kwashe kayanku’. Ga shi nan dai! A ranar 29 ga Mayu, jihar Zamfara za ta
shaidi wani sabon fuska da sabon farawa – gwamnatin Dauda Lawal.
Daga cikin abubuwa masu girgizarwa a zabukan 2023
a Nijeriya akwai guguwar tsunami ta siyasa da ta kawo karshen mamayar sama da
shekaru goma na gaggan ‘yan siyasa a siyasar jihar Zamfara. Dukkanin
manya-manya wadanda ake kambama kimar siyasarsu sun hada karfi da karfe a sansani
guda a karkashin inuwar jam'iyyar APC, a karon farko tun bayan komawar mulkin
dimokuradiyya da jam'iyyar PDP ta karya lagon cin zabe a jihar Zamfara.
Tsoron zama a jam'iyyar
adawa ta PDP ne ya sa Gwamna mai barin gado, Bello Matawalle ya yanke shawarar
sauya sheka daga jam'iyyar zuwa APC mai mulki, cike da fatan gwamnatin Tarayya za
ta kubutar da shi, bugu da kari, a kuma dakatar da duk wani dan siyasa daga
jam'iyyar yin takara.
Hasashen Matawalle kamar
na mayaki shi kaɗai ne a cikin yaƙi da ƙwararru da gogaggun mayaka. Wani mataki
ne na tsoro da zakuwa domin kaucewa murkushewar hadakar mutum biyu na Abdulaziz
Yari da Kabiru Marafa ya sanya shi daukar matakin yarinta na sauya sheka - komawar
da ta kusan tsaga jam'iyya mai mulki a jihar, amma zakuwa, son kai, da kuma
yunwar mulki ta sa aka yi nasarar wannan auren na daidaito da gwamna mai barin
gado da kuma wadanda ake kira jaruman jam’iyya.
Manazarcin siyasa zai
gaya maka cewa kawancen da aka yi a Zamfara na APC tunda fari an yi shi bisa
rashin fahimta saboda kwadayi da hassada da neman mulki. Burin Matawalle shi ne
tabbatar da takararsa ta biyu; Burin Abdulaziz Yari shi ne ya tabbatar da samun
nasarar kujerarsa ta Sanata; Haka ma ga Sanata Kabiru Garba Marafa, yaki ne na neman
kujerar Sanatan tsakiya.
Dukkanin
wannan lissafe-lissafe na siyasa da kuma murda-murdar siyasa an tsara su ba
tare wani daga cikin masu wannan tsare-tsaren sun yi la’akari ko kuma ganin
Dauda Lawal a matsayin barazana ba. Suna ɗaukarsa a matsayin dan koyo wanda da ƙyar
ya kwaci kansa daga dambatawa da su.
A yayin da rikicin
jam’iyyar APC ya lafa, Gwamna Matawalle ya shiga jam’iyya mai mulki, aka yi
sulhu da ‘karfi’ da Abdulaziz Yari da Marafa; Sai da gwamnatin tarayya da duk
masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC suka shiga tsakani domin hadakar ta tabbata.
Babu wani daga cikin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a matakin kasa da jiha da
yake da hangen nesan daukar Dauda Lawal a matsayin barazana. Zamfara ta samu, haka
suka yi imani.
Bisa ga wannan yanayi,
tsohon babban ma’aikacin bankin ya yanke shawarar sauya sheka zuwa jam’iyyar
PDP, wanda wannan ya kasance mafarin sabon yanayi a tarihin siyasar jihar.
Gwamnan, jam’iyyar APC a matakin jiha da kasa, suka yi raha game da sauya
shekar. Yari da Marafa suka yi takamar cewa sune ‘masu’ siyasar Zamfara.
Gwamna mai barin gado
ne ya gane kololuwar dacewar siyasar Dauda a daidai lokacin da ‘bakin alkalami
ya riga ya bushe’. Yanayin siyasar jihar ya kara zafi ne bayan zaben fidda
gwani na gwamna na jam'iyyar PDP a watan Mayun 2022 wanda ya samar da Dauda
Lawal a matsayin wanda ya yi nasara.
A lokacin ne gwamnan ya
lura da kuskuren da ya yi na rashin kara Dauda a cikin jerin wanda zai ‘tare
masa hanya’. An yi ta rade-radin cewa Gwamna Matawalle ne ya dauki nauyin wani fusataccen
dan takarar gwamna, Shehu Bakauye, domin ya nuna rashin amincewa da yadda
jam’iyyar PDP ta gudanar da zaben fidda gwani.
Kasancewar Dauda a
fafatawar, Gwamna Matawalle ya yi hasashen za a samu koma baya a sake zabensa,
duk da cewa Yari da Marafa suna ta tausasa shi da fata na karya.
Duk da haka, zuciyar
Matawalle ta ci gaba da ingiza shi da ya yi amfani da kotu domin dakile damar
Dauda. Mun shaida yadda wani Alkalin wata babbar kotun tarayya da ke Gusau ya
yi rawa ga kidar da gwamnan ya yi, inda a lokuta daban-daban guda biyu ya soke
zaben fidda gwanin da ya samar da Dauda Lawal.
Kotun daukaka kara da
ke zamanta a Sakkwato, a hukuncin da ta yanke, ta mayar da Dauda Lawal a
matsayin wanda ya yi nasara. Hukuncin da ya karawa Dauda kuzari ya kuma kasance
koma baya ga Matawalle da APC.
A cikin kasa da wata
guda, sunan Dauda Lawal ya zama abin ambato a gidaje a kauyuka da garuruwa a
fadin jihar. Shahararriyar motar kamfen din ‘Bazamfara’ ta yi barna sosai a
yunkurin Matawalle na sake ganin an zabe shi a takararsa ta biyu fiye da
kokarin da Yari da Marafa suka yi wajen ganin ya samu nasara.
Lawal ya ji daɗin tumbatsar
farin jininsa a ranar. Salonsa, dagewarsa, da sahihancinsa na siyasa ya ba shi
babban kima. A karon farko a tarihin jihar, dan takarar gwamna ya kaddamar da
yakin neman zabensa tare da kaddamar da manufofinsa.
Manufofin Lawal mai
dauke da nagartattun kudurori shida ya sanyawa mutane fatan cewa wani sabon mai
jini a jika ya shiga fafatawar domin ceto. Taken yakin neman zabensa, ‘Ceto da
Gina Zamfara,’ ya fallasa gaskiyar jihar.
Dauda ya yi yakin neman
zabe a daukacin kananan hukumomin jihar 14 ba tare da tara ‘yan daba ko jama’ar
haya ba. A kafatanin lokacin yakin neman zabe, Lawal ya nuna matukar kamun kai
da rashin son ‘yan bangar siyasa. Ya kan roki ‘yan sanda da su kare allunan
talla da tutocin ‘yan adawa daga taron masu zumudi. Na shaida hakan a wurare da
yawa.
A takaice dai, ina
bayyanawa jama’a cewa dukkanin wadanda ake kira da ‘jiga-jigai’ a Zamfara; ko
ya kasance Yari ne ko Yarima; Marafa ko Matawalle; Shinkafi ko Jaji duk sun yaki
Dauda da dukkan karfinsu, amma ba su yi nasara ba. Kada a yaudare ku!
Bala ya rubuto ne daga
Gusau kuma za a iya samunsa ta isbdaurawa@gmail.com
Fassarar Muhammad A.
Abubakar
No comments