Daga Wakilinmu Gwamnatin jihar Bauchi ta gayyaci Dr. Idris Dutsen Tanshi domin zuwa ya kare kansa bisa zargin '6atanci'...
Daga Wakilinmu
Gwamnatin jihar Bauchi ta gayyaci Dr. Idris Dutsen Tanshi domin zuwa ya kare kansa bisa zargin '6atanci' ga Annabi Muhammadu (SAW).
Sanarwar ta fito ne a wata takarda daga Hukumar shari'a ta jihar Bauchi wanda Shugaban hukumar, Ibrahim Musa Yisin ya sanyawa hannu kuma Jaridar MADOGARA ta samu kwafinta.
Takardar ta fara da cewa; "Bisa umurni ina rubuto maka gayyata a hukumance zuwa ga wata tattaunawa (munakasha) domin karin bayani kan wasu kalamai da ka yi a lokacin Tafsirin Ramadan idan ka ce; "Kai! Na Manzon Allahn ma ba mu son taimakonsa karewarta ke nan".
Takardar ta ci gaba da cewa; "Gamsasshen karin bayaninka zai taimaka wajen rage tashin hankalin da al'ummar Musulmi ta fada (sakamakon kalamanka), tare da samar da dawwamammen zaman lafiya a tsakanin al'ummar Musulmi".
Ibrahim Musa Yisin ya tabbatar da cewa za a gudanar da zaman wannan tattaunawar ne a ranar Asabar 8 ga watan Afrilun 2023 da misalin karfe 10 na safe a DEC (Development Exchange Centre) dake titin Ahmadu Bello Way dake Bauchi.
A karshe hukumar ta shawarci Malamin da ya daure ya halarci zaman.
Ga kwafin takardar;
No comments