*Almajiransa sun yi barazanar tarwatsa zaman lafiyar Nijeriya *Yadda kare martabar Manzon Allah (S) ke neman juyewa zuwa fadan akida Dag...
*Almajiransa sun yi barazanar tarwatsa zaman lafiyar Nijeriya
*Yadda kare martabar Manzon Allah (S) ke neman
juyewa zuwa fadan akida
Daga Muhammad Farouk
Ana ci gaba da mayar da
kausasan martani a tsakanin Malaman addinin Musulunci a cikin watan Ramadan
dangane da zargin da ake yi wa wani Malami dan kungiyar Salafiyya dake garin
Bauchi, Sheikh Abdul’aziz Idris Dutsen Tanshi.
Zargin ya samo ne
dangane da wata kalma da Shehin Malamin ya gayawa Manzon Allah a yayin da yake
mayar da martani ga wata waka da aka yi wa Manzon Allah (S). Lamarin dai ya
jawo cece kuce a tsakanin al’ummar Musulmi wanda ta kai ga Malamai da dalibai
da sauran gama garin al’umma ke ta kira ga gwamnatin jihar Bauchi da ta kama
Malamin tare da yi masa tittsiye.
Sai dai da dukkanin
alamu lamarin kare martabar ta Manzon Allah (S) ya juye ya koma fadan akida, a
inda bangaren Izala/Salafiyya suke kallon lamarin a matsayin bangaren Darikun
Sufaye da Shi’a na yakar akidarsu ne lamarin da dukkanin bangarorin suka
musanta.
Bayanai da rahotanni da
suka bayyana a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wasu Malamai bangaren Izala
da Salafiyya suka barranta wadannan kalamai na Dr Abdul’aziz Idris Dutsen
Tanshi. A yayin da mafi yawan Malaman Izala da Salafiyya fitattu a Arewacin
Nijeriya suka nuna goyon bayansu ga da’awar ta Dr Abdul’aziz Idris Dutsen
Tanshi lamarin da ya sake fusata al’ummar Musulmi.
A ranar 6 ga watan
Afrilun 2023, Gwamnatin jihar Bauchi ta gayyaci Dr. Idris Dutsen Tanshi domin zuwa ya kare kansa bisa
zargin 6atanci' ga Annabi Muhammadu (SAW).
Sanarwar ta fito ne a
wata takarda daga Hukumar shari'a ta jihar Bauchi wanda Shugaban hukumar,
Ibrahim Musa Yisin ya sanyawa hannu kuma Jaridar MADOGARA ta samu kwafinta.
Takardar ta fara da
cewa; “Bisa umurni ina rubuto maka gayyata a hukumance zuwa ga wata tattaunawa
(munakasha) domin karin bayani kan wasu kalamai da ka yi a lokacin Tafsirin
Ramadan idan ka ce; "Kai! Na Manzon Allahn ma ba mu son taimakonsa
karewarta ke nan".
Takardar ta ci gaba da
cewa; “Gamsasshen karin bayaninka zai taimaka wajen rage tashin hankalin da
al'ummar Musulmi ta fada (sakamakon kalamanka), tare da samar da dawwamammen
zaman lafiya a tsakanin al'ummar Musulmi".
Ibrahim Musa Yisin ya
tabbatar da cewa za a gudanar da zaman wannan tattaunawar ne a ranar Asabar 8
ga watan Afrilun 2023 da misalin karfe 10 na safe a DEC (Development Exchange
Centre) dake titin Ahmadu Bello Way dake Bauchi.
A karshe hukumar ta
shawarci Malamin da ya daure ya halarci zaman.
Aikawa da wannan
takarda ke da wuya, Dr Abdul’aziz Dutsen Tanshi a yayin gabatar da Tafsirin
Ramadan cikin kwarin guiwa ya ce a shirye yake ya halarci wannan zaman
tattaunawar domin “ni kadai gayya”, inji shi a wani faifan bidiyo da shafin da
ake yada karatuttukansa suka wallafa.
Sai dai fitar wannan
sako ke da wuya a washegari, kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a wa’ikamatus
Sunnah (JIBWIS) reshen jihar Bauchi ta ce ta janye halartar zaman da za a yi da
Dr. Idris Dutsen Tanshi, tana mai cewa; kamata ya yi a yi wa Malamin nasiha
idan ana ganin ya yi amfani da wasu lafuzan da bai kamata ba. Domin a cewar
JIBWIS zantukan Malamin kan Manzon Allah (S) batu ne da ya shafi akidarsu.
Iliyasu Danjuma Bandas,
Sakataren JIBWIS na Bauchi shi ne ya tabbatar da hakan a takardar da ya aikewa
da Hukumar Shari’a ta Bauchi kan batun janyewarsu daga halartar zaman
tattaunawar mai dauke da kwanan wata 7 ga watan Afrilun 2023.
“Da fatan za ka fahimce
mu, kuma Allah ya yi mana kyakkyawan jagora, Amin”, a cewar bayanin takardar.
A wannan ranar an ga
ganga-gangar gamayyar taron Malaman Izala/Salafiyya daga garuruwa daban-daban
da ya hada da Kano, Zamfara Kaduna da sauran su suka dira a garin Bauchi a inda
Malamin yake gabatar da jawabi domin ba shi kariya.
Jaridar MADOGARA ta
labarto cewa; almajiran Sheikh Dr Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi dake garin
Bauchi, sun bayyana cewa su a shirye suke su mutu da wani abu ya taba farcen
Malaminsu. Malam Abdallah wanda ya zo daga Kano shi ne wanda ya bayyana hakan a
madadin almajiran Shehin Malamin a daren ranar Juma’a a Masallacin Malamin dake
Bauchi.
A yayin da Malam
Abdallah ke wannan bayanin, almajiran Shehin Malamin dake cikin Masallacin sun
rika kwantsama kabbara suna mai jaddada abin da Malam Abdallah ya fadi a yayin
da Dr Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ke gefe yana saurarensu.
Malam Abdallah ya ci
gaba da cewa; “duk wanda ya ci mutuncin Malam, na rantse da Allah rigimar
addini ce za ta barke wacce babu ranar da za a toshe ta”, nan take mahalarta a
masallacin suka barke da kabbara mai karfi.
“Ba wani dan sanda da
ya kira, Ubangiji ne kawai ya sanya min a raina cewa mutanen nan wulakantaka
suke son su yi. So suke su tozartaka”, inji Malam Abdallah a gaban Dr Idris
Dutsen Tanshi.
A don haka Malam
Abdallah ya tabbatar da cewa Malaminsu Dr Idris Dutsen Tanshi ba zai halarci
zaman tattaunawar da hukumar shari'a ta jihar Bauchi ta shirya ba. Ya kuma
tabbatar da cewa fahimtar Malamin na su ita ce akidarsu.
Dr Idris Dutsen Tanshi
har wala yau a jawabinsa a wannan dare a gaban almajiran na shi ya yi zargin
cewa ana shirin kai shi gidan yari da rusa masa masallacinsa, inda ya ce; “ya
ce wallahi Malam abin da ake nufi da maganar mukabala din nan; bayan mukabala
ana son a kama ka. Bayan an kama ka za a kai ka kotu, ana kai ka kotu, Alkalin
zai tura ka gidan gyaran hali, idan ya tura ka gidan gyaran hali daga baya
masallacinka za a rusa shi”, inji shi a lokacin da yake labarta abin da wani ya
gaya mishi.
Wadannan kalamai na
tunzuri ya sanya a wata sabuwar sanarwa da Hukumar Shari’a ta Bauchi ta fitar,
wanda shugabanta Ibrahim Musa Yisin ya sanyawa hannu ya ce sun dage zaman
tattaunawar na ranar Asabar 8 ga watan Afrilu, za su sanar da sabuwar ranar da
za su yi zaman tattaunawar.
“ina mai sanar da kai a
hukumance cewa an sauya ranar gabatar da wannan tattaunawar kamar yadda aka
tsara a ranar 8 ga watan Afrilun 2023.
“Za mu sanar da kai
sabuwar ranar da za a sanya yadda ya dace”, sanarwar ta tabbatar.
Hukumar shari’a ta
yanke wannan hukunci ne bayan tabbatar da cewa gamayyar Malamai da almajirai
masu goyon bayan Dr Idris Dutsen Tanshi daga bangaren Izala da Salafiyya sun
dira a masallacin Malamin domin ba shi kariya tare da jaddada goyon bayansu ga
kalaman Malamin tare da shelanta kalaman tashin hankali.
Har wala yau a wata
takarda da hukumar shari’a ta Bauchi ta fitar mai dauke da kwanan wata 12 ga
watan Afrilun 2023, ta bayyana cewa ta karbi dukkanin korafe-korafe daga
bangarori daban-daban za ta sanar da sabon matakin da za ta dauka wanda zai
wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.
Har wala yau Kwamishinan
Shariah na jihar Bauchi mai suna Malam Mustapha Baba Ilela, ya yi bayanin yadda
lamarin ya kasance tunda fari da kuma yadda a karshe Æ´an'uwan Dr Abdul’aziz
Dutsen Tanshi a akida wato bangaren Izala da Salafiya suka canzawa lamarin wata
fuska ta daban ya koma kamar fadar kungiyanci.
Wannan lamari ya soma
aukuwa ne a yayin da Dr Idris Dutsen Tanshi yake mayar da martani kan wani
waken yabo na fiyayyen halitta da wasu ‘yan wasan Hausa suka yi wanda aka fi
saninsu da ‘yan Kannywood, Shehin Malamin ya ce; "Kai! Na Manzon Allahn ma
ba mu son taimakonsa karewarta ke nan".
Yanzu dai ya zuwa hada
wannan rahoton, bangaren Izala/Salafiyya suna kallon lamarin a matsayin yaki da
akidarsu ba wai kare martabar Manzon Allah (S) ba, a yayin da bangaren sauran
al’ummar Musulmi ke kallon abin a matsayin dole a tashi a yaki masu taba
janibin Manzon Allah (S) da sunan Tauhidi ta hanyar gaya wa Manzon Allah (S)
magana, izgili ko gatse.
No comments