Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

3 Mayu: Majalisar Dinkin Duniya Ta Nuna Damuwa Kan Cin Zarafin 'Yan Jarida

  Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da damuwa kan yadda yancin jarida ke fuskantar tasgaro daga kowane lungu tsako na duniya, saboda yadda ak...

 


Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da damuwa kan yadda yancin jarida ke fuskantar tasgaro daga kowane lungu tsako na duniya, saboda yadda ake ci gaba da cin zarafin ‘yan jaridu, ta hanyar tsare su ko ma kashe su a kasashe da dama.

Da yake jawabi a jajiberen ranar 'yancin 'yan jaridu ta duniya dake gudana kowace uku ga watan Mayu, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya koka kan hakkin 'yan jaridu da kafafen yada labarai na duniya.

Yayi jawabi ne a wani taron da aka gudanar a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York, inda yace “’yan jaridu na fuskantar cin zarafi a kowane lungu na duniya”

"Dukkan 'yancinmu ya dogara ne ga 'yancin 'yan jarida,"

Cibiyar UNESCO ta ba da lambar yabo ta 'yancin 'yan jarida ta duniya ta wannan shekara ta 2023 ga mata uku 'yan Iran, 'yan jarida biyu da wani mai rajin kare hakkin bil'adama, wadanda aka daure.

'Yan jaridun Iran

Wadanda suka samu lambar yabo ta UNESCO sun hada da 'yan jaridar Iran Elaheh Mohammadi da Niloufar Hamedi, wadanda suka taimaka wajen fallasa mutuwar Mahsa Amini a watan Satumba, da kuma mai fafutukar kare hakkin bil'adama Narges Mohammadi.

Guterres dai bai ambaci wata kasa kai tsaye ba kan cin zarafin ‘yan jarida, amma wasu kafafafen yada labarai sun yi tsokaci kan wasu mutane, kamar dan jaridar Wall Street Journal Evan Gershkovich, wanda aka tsare a Rasha kan zargin leken asiri da ya ki amincewa.

"Yaƙin neman 'yancin 'yan jarida da kuma neman sakin Evan yaƙi ne don 'yancin kowa," in ji mawallafin Wall Street Journal Almar Latour.

Dan jaridar Rasha

Kafofin yada labarai da dama sun yi tir da tuhume-tuhumen da ake yi wa Gershkovich da cewa ba shi da tushe balle makama, yayin da shugaban Amurka Joe Biden ya kira daurin da aka yi masa a matsayin "babu ka'ida ba."

Mawallafin jaridar New York Times A.G. Sulzberger ya ce ba wai danniya kai tsaye kadai ke barazana ga 'yan jarida ba, hatta ga 'yancin samun bayanai.

Ita kuwa shugabar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, Agnes Callamard, cin zarafi ya zama ruwan dare gama duniya a halin yanzu.

Kisan 'Yan jaridu

A cewar kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta Reporters Without Borders, akalla ‘yan jaridu 55 da wasu ma’aikatan yada labarai hudu aka kashe a bakin aiki a shekarar 2022.

-RFI Hausa

No comments