Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Aisha Buhari Ta Roƙi A Kawo Karshen Yaƙin Sudan

Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta roƙi a haɗa karfi da karfe don ganin kurar rikicin Sudan ta kwanta. Jaridar Premium Times ta Na...


Uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta roƙi a haɗa karfi da karfe don ganin kurar rikicin Sudan ta kwanta.

Jaridar Premium Times ta Najeriya ta ruwaito Aisha Buhari na wannan kira a wani taro da ta jagoranta jiya Litinin a fadar gwamnati da ke Abuja.

A cewar jaridar, Aisha Buhari na ganin akwai rawar da matan shugabannin Afirka za su iya takawa musamman wajen kai agaji Sudan.

Tun ranar 15 ga watan Afrilu, yaƙi ya ɓarke a Sudan kuma har wannan lokaci, an kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin.

Sama da mutane 500 ake kyautata zaton cewa rikicin ya yi sanadin sun rasuwarsu kawo yanzu.

No comments