Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Albashina 942,000 Ne A Wata, Alawus Ɗin Bai Taka Kara Ya Karya Ba – Ngige

Yayin da ake ta kiraye-kirayen a ƙara mafi ƙarancin albashi na N30,000 a Najeriya, ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngig...


Yayin da ake ta kiraye-kirayen a ƙara mafi ƙarancin albashi na N30,000 a Najeriya, ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ya ce albashinsa da na sauran ministoci bai fi N942,000 ba.

Da yake magana a wani shirin 'Siyasar mu a Yau' na gidan talbijin ɗin Channels, Ngige ya kuma ce ba su da alawus-alawus a matsayinsu na ministoci, sai alawus ɗin aiki kawai.

“Duk ministan da ka gani, shi ne abin da yake samu, masu ba da shawara na musamman su ma suna samun kusan wannan adadin.

Alawus ɗin bai taka kara ya karya ba, ba mu da wani alawus, sai idan za mu yi tafiya. Kuna iya samun alawus ɗin hutu kamar duk wani jami'in gwamnati," in ji Ngige.

Ya kara da cewa a baya-bayan, an sake bitar kuɗaden alawus ɗin tafiye-tafiye na ministoci tare da na manyan sakatarori da sauransu.

“An ƙara kuɗin zuwa N100,000 ga minista, na ƙaramin minista kuma zuwa N75,000, sai kuma na manyan sakataror N70,000, an ƙara na kowa, ba namu kaɗai ba,” a cewarsa.

Da aka tambaye shi ko me ya sa gwamnati ta kasa magance batun rashin aikin yi a ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 33.3 a shekarar 2021, Ngige ya ce samar da ayyukan yi wani nauyi ne da ya rataya a kan kamfanoni, ba wai gwamnati kaɗai ba.

Ya kuma ɗora alhakin ƙaruwar rashin aikin yi, a kan raguwar zuba jari daga ƙasashen waje.

No comments