A yau Lahadi Turkiyya ke gudanar da zaben da ka iya tsawaita wa’adin mulkin shugaba, Recep Tayyip Erdogan, wanda ya shafe shekaru 20 yana ja...
A yau Lahadi Turkiyya ke gudanar da zaben da ka iya tsawaita wa’adin mulkin shugaba, Recep Tayyip Erdogan, wanda ya shafe shekaru 20 yana jagorancin kasar.
Zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisar dokoki ya rikide zuwa wat kuri’ar jin ra’ayin al’umma a kan shugaban Turkiyya mafi dadewa kan karagar mulki da jam’iyyarsa, kuma shine mafi sarkakiya daga cikin zabukan da shugaba Erdogan ya taba fuskanta, inda wasu ke gaanin yana iya faduwa.
Erdogan mai shekaru 69, ya jagoranci kasar mai yawan al’umma miliyan 85 zuwa ci gaba da aka dade ba gani ba a cikin shekaru 100 na bayan daular Usmaniyya.
Irin tasirin da Turkiyya ta yi a harkokin da suka shafi Turai da Gabaas ta Tsakiya a ‘yan shekarun baya bayan nan matsayin na daya daga cikin mambobin kungiyar tsaro ta NATO ya sa wannan zabe ya kasance da mahimmaci ga Amurka da Tarayyar Turai, kamar yadda yake ga Turkiyar kanta da Rasha.
No comments