Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum 176 A DRC

  Hukumomi a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo sun ce adadkin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa ...

 


Hukumomi a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo sun ce adadkin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar ƙasa ya kai 176.

Gwmannan Kudancin Kivu ya ce har yanzu akwai ƙarin mutanen da ba a ƙirga ba, waɗanda ake fargabar sun nutse a cikin ƙasa.

Ƙauyukan Bushushu da Nyamukubi sun tafi babu komai a cikinsu, sakamakon kogunan da suka cika suka batse a yankin gabashin ƙasar.

An samu rahoton zabtarewar ƙasa da ta lalata gidaje da gine-gine masu yawa.

Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun rawaito cewa sama da kashi uku na wani ƙauye ya ruhse ciki har da makarantu da kuma cibiyoyin lafiya.

No comments