Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

An Harbawa Haramtacciyar Kasar Isra'ila Makaman Roka Bayan Kashe Bafalasdine

  Wani Bafalasdine da ke yajin cin abinci ya mutu a hannun Haramtacciyar kasar Isra'ila, kusan watanni uku bayan tsare shi sakamakon zar...

 


Wani Bafalasdine da ke yajin cin abinci ya mutu a hannun Haramtacciyar kasar Isra'ila, kusan watanni uku bayan tsare shi sakamakon zargin yana da alaka da masu tayar da kayar baya, lamarin da ya janyo suka daga kasashen Larabawa ga Isra'ila da kuma hare-haren roka daga Gaza kamar yadda RFI Hausa ta labarto.

Mutuwar Khader Adnan ta sanya an harba rokoki guda uku wanda mayakan Gaza suka harba, wadanda suka fada a yankin haramtacciyar kasar Isra’ila, sai dai ba a samu asarar rai ba.

Firaministan Falasdinu Mohammad Shtayyeh ya bayyana mutuwar Adnan, wanda aka kama a yammacin gabar kogin Jordan, a matsayin kisan gilla da gangar.

Adnan, mai shekaru 45, shi ne Bafalasdine na farko da ya mutu sakamakon yajin cin abinci, a cewar kungiyar fursunonin Falasdinu.

Wasu daga cikin Falasdinawan da ake tsare da su sun mutu ne sakamakon yunkurin tilasta musu cin abinci, in ji Daraktan kungiyar, Qaddura Faris.

Falasdinawa sun rufe shaguna yayin da suke gudanar da yajin aikin gama-gari a garuruwan Yammacin Kogin Jordan sakamakon mutuwar Adnan.

No comments