Daga Ammar M. Rajab Rahotannin dake shigo ma Jaridar MADOGARA na nuni da cewa Allah ya yi wa Muhammad Ibrahim Yareema rasuwa. Mu...
Daga Ammar M. Rajab
Rahotannin dake shigo ma Jaridar MADOGARA na nuni da cewa Allah ya yi wa Muhammad Ibrahim Yareema rasuwa.
Muhammad ya kasance ƙani ne kuma ɗan uwa na jini ga abokin Aikinmu, Ali Ibrahim Yareema.
Ali Ibrahim Yareema yana ɗaya daga cikin mashawartan wannan jarida.
Muhammad Ibrahim Yareema ya rasu ne sakamakon hatsari da ya yi da safiyar yau Juma'a 12 ga watan Mayun 2023 akan hanyarsa ta dawowa daga ɗaurin auren abokinsa da aka ɗaura a ƙauyen Gabari.
Sauran da hatsarin ya rutsa da su an garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu. Amma shi da ya riga ya rasu.
No comments