Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ana ci gaba da gwabza yaƙi a Sudan duk da yunƙurin tsagaita wuta

  Rundunar sojin Sudan da dakarun tsaro na RSF na ci gaba da gwabza faɗa domin ƙwace iko da muhimman wurare a Khartoum babban birnin ƙasar, ...

 


Rundunar sojin Sudan da dakarun tsaro na RSF na ci gaba da gwabza faɗa domin ƙwace iko da muhimman wurare a Khartoum babban birnin ƙasar, duk kuwa da yunƙurin tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin da ke yaƙi da juna.

Ana sa ran gudanar da tattaunawar sulhun tsakanin ɓangarorin biyu a ƙasar Saudiyya, kuma duka ɓangarorin biyu sun aike da wakilansu.

Kawo yanzu dai babu tabbacin fara tattaunawar da ƙasashen Saudiyya da Amurka suka ɗauki nauyin jagoranta.

Wakilin BBC da ke Afirka ya ce ana ganin hayaƙi na tashi a sararin samaniyar birnin Khartoum.

Ana kuma jin ƙarar harbe-harbe da jiragen yaƙi a yankunan da ke hannun dakarun RSF ciki har da fadar shugaban ƙasar.

Fiye da mutum miliyan bakwai da ke zaune a Khartoum ne suka maƙale a birnin, suke kuma fama da ƙarancin abinci da ruwan sha da magunguna.

Mutanen na cike da fatan tattaunawar tsagaita buɗe wuta da Amurka da Saudiyya ke jagoranta za ta kawo ƙarshen yaƙin.

No comments