Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Taron Shugabannin Larabawa Ya Maida Hankali Kan Siriya, Falasdinu, Yemen Da Sudan

A karshen taron koli na Jeddah da aka gudanar a kasar Saudiyya, kungiyar kasashen Larabawa ta yi maraba da komawar Syria shiga tarukan majal...


A karshen taron koli na Jeddah da aka gudanar a kasar Saudiyya, kungiyar kasashen Larabawa ta yi maraba da komawar Syria shiga tarukan majalisar kungiyar, tare da bayyana fatanta na ganin cewa hakan ya taimaka wajen tallafawa zaman lafiyar kasar ta Syria da kuma kiyaye yankinta.

A cikin "Sanarwar Jiddah", kungiyar hadin kan Larabawa ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan ayyuka da cin zarafi da ake yi wa Falasdinawa da rayukansu da dukiyoyinsu, tare da jaddada muhimmancin kara zage damtse wajen cimma matsaya mai cike da adalci ga Palasdinawa.

Sannan dole a samar da hanya don samun zaman lafiya a kan tsarin samar da kasashe biyu bisa ga shirin zaman lafiya na Larabawa da kudurori na kasa da kasa, Ka'idoji da dokokin kasa da kasa.

A cikin "Sanarwar Jiddah", kungiyar hadin kan Larabawa ta tabbatar da cewa tana bibiyar abubuwan da ke faruwa a halin da ake ciki a Jamhuriyar Sudan, inda ta bayyana matukar damuwarta game da illar da rikicin ya haifar kan tsaro, da zaman lafiyarta.

No comments