Daga dama: zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da Gwamna Wike na Ribas a yayin ziyarar kaddamar da ayyukan a jihar Ribas. Zababb...
![]() |
Daga dama: zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, tare da Gwamna Wike na Ribas a yayin ziyarar kaddamar da ayyukan a jihar Ribas. |
Zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin yi wa kasa ayyukan ci gaba daidai-wa dai da ba tare nuna wariya ga wani bangare ba.
Asiwaju Tinubu, wanda
za a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, ya bayyana
hakan ne a ranar Laraba a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da ofishin zababben shugaban kasar ya fitar dauke da sa hannun Abdulaziz Abdulaziz a ranar Laraba.
Zababben shugaban kasar
yana ziyarar kwanaki biyu ne a jihar domin kaddamar da ayyukan da gwamnatin
Nyesom Wike ta aiwatar.
“Ba zan mayar da wani
yanki saniyar ware ba, amma zan bar ayyukan da ba za a manta da su ba a fadin Nijeriya,”
in ji shi a yayin bude gadar Rumuokwuta/Rumuola.
Tinubu ya yabawa Gwamna
Wike bisa ayyukan ci gaba da ya cimma a jihar Ribas, musamman gadar sama 12 da
aka gina a fadin babban birnin jihar, inda ya ce lallai tarihi zai rika tunawa
da shi.
Ya ce da irin nasarorin
da ya samu a jihar, Nijeriya za ta bukaci gwamnan Ribas din mai barin gado a
manyan mukamai.
A bangaren siyasa,
Tinubu ya godewa Wike da al’ummar jihar Ribas bisa goyon bayan da suka ba shi.
Ya ce yana jihar ne bisa
alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe a Ribas, inda ya ce “idan ka
yi alkawari, ka cika shi.
“Ba zan taba mantawa da
muhimmiyar rawar da manya da kuma al’ummar jihar nan suka taka ba a yakin neman
zaben da na yi na zama shugaban kasar nan. Kuna da godiyata ta har abada.
“A mai girma Gwamna
Wike, na ga mutum mai ka’ida. Ya dauki matakin da ya dace na cewa a mayar da shugabancin
kasarnan Kudu, kuma ya samu kwarin guiwar jajircewa kan matsayarsa, ba tare da
la’akari da wa hakan zai batawa ba.
“Hakika shi mutum ne
mai mutunci. Bai zabi biyan bukatar kansa ba, a’a, ya zabi biyan bukatar kasa
da al’ummar jihar Ribas, ina gode masa bisa wannan jagorancin na sadaukar da
kai,” inji shi.
A nasa jawabin, Wike ya
ce gayyatar da aka yi wa Tinubu domin kaddamar da ayyuka a jihar cika alkawari
ne da aka yi a ziyarar yakin neman zaben shugaban kasa a Ribas.
Ya kuma godewa Tinubu kan yadda ya amince ya ziyarci
jihar Ribas tare da kaddamar da ayyukan.
Wike, wanda ya caccaki
shugabannin jam’iyyarsa ta PDP, ya yaba da zaben Tinubu wanda a cewarsa, ya
kunyata masu zagon kasa.
Taron ya samu halartar
Kakakin majalisar wakilai Hon. Femi Gbajabiamila da Gwamna Abubakar Badaru
(Jigawa), David Umahi (Ebonyi), Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Seyi Makinde
(Oyo) da Hope Uzodinma (Imo).
Sauran sun hada da tsoffin
gwamnoni Dr Peter Odili (Ribas), Cif Bisi Akande (Osun), Cif James Ibori
(Delta), Dr Kayode Fayemi (Ekiti), Cif Timipre Sylva (Bayelsa) da Cif Ayo
Fayose (Ekiti).
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da zababben gwamnan jihar Ribas, Mista Sim Fubara, Ministan matasa da ci gaban wasanni, Mista Sunday Dare, Mista Dele Alake da kuma Alhaji Kashim Ibrahim Imam, da dai sauransu.
No comments