Barcelona ta lashe Gasar La Ligarta ta farko tun kakar wasanni ta 2018-19, saura wasa huɗu a kammala gasar, bayan wata nasara mai cike da ƙa...
Barcelona ta lashe Gasar La Ligarta ta farko tun kakar wasanni ta 2018-19, saura wasa huɗu a kammala gasar, bayan wata nasara mai cike da ƙayatarwa a gidan Espanyol, abokan hamayyarsu na birnin.
Barca ta ci ƙwallo 3-0 a rabin lokaci, inda Robert Lewandowski ya ci ƙwallonsa na 20 a kakar bana, kafin Alejandro Balde, matashi ɗan shekara 19, ya ninka ratar da suka bayar a wasan.
Lewandowski ya ƙara ƙwallo na uku kafin Jules Kounde ya danƙara ƙwallo na huɗu da ka a raga.
Espanyol ta rage tazarar da aka ba ta, ta hanyar ɗan wasanta Javier Puado da Joselu, sai dai sun ci gaba da kasancewa cikin matsala inda suke a can kusa da ƙasan tebur.
Barcelona tana da maki 85, wato maki 14 tsakaninta da babbar abokiyar hamayyar da ke biye mata a tebur Real Madrid, da sauran wasannin da za a ƙare da maki 12.
Ita ce nasarar ɗaukar Gasar La liga ta farko ga Barcelona tun bayan tafiyar gwarzon kulob ɗin Lionel Messi a watan Agustan 2021, kuma ta farko tun bayan naɗa Xavi a matsayin kocin ƙungiyar a watan Nuwamban 2021.
A lokaci guda kuma, Espanyol na cikin hatsarin faÉ—awa raligeshin na biyu daga Gasar La liga a cikin kakar wasa huÉ—u, bayan rashin nasara karo na tara a karawa 11.
Maki huÉ—u ne ratar su da raligeshin, yayin da rage saura wasa huÉ—u.
'Yan wasan Barcelona sun sha murna a cikin fili bayan sun lashe gasar La ligarsu ta 27
Kwalliya ta biya kuÉ—in sabulu ga Xavi a cikakkiyar kakar wasansa ta farko
Sai ‘yan wasan Barcelona sun yi jira, kafin su É—ora hannuwansu a kan kofin La ligar, amma dai sun yi murna sosai bayan an busa tashi, sannan suka fice daga filin cikin sauri lokacin da wasu magoya bayan Espanyol sun dira cikin fili.
Barca sun kasance a bayan Real Madrid da ratar maki uku lokacin da suka yi rashin nasara a gidan Madrid da ci 3-1 ranar 16 ga watan Oktoba, daidai lokacin da cikin ban takaici aka fitar da su daga Gasar Zakarun Turai bayan sun yi rashin nasarar wasa uku cikin shida a rukuni.
Sai dai Xavi, wanda ya lashe gasar La ligarsa ta takwas a lokacin ƙasaitaccen zaman da ya yi na shekara 17 a kulob ɗin, ya yi nasarar ɗaukar gasar a cikakkiyar kakar wasansa ta farko a matsayin kocin ƙungiyar.
Dare ne mai cike da shauƙi musamman dai ga kaftin Sergio Busquets, wanda ya tabbatar da zai bar Barcelona a ƙarshen kakar bana, bayan ya shafe tsawon shekara 18 a kulob ɗin.
Wannan ce Gasar La liga ta tara da É—an wasan mai shekara 34 ya ci da Barca, kuma lamarin ga dukkan alamu na cike da armashi ga Æ™ungiyar wadda, matasan ‘yan wasanta Balde da Kounde suka jefa Æ™wallayensu na farko a gasar La Liga da jesin Barcelona.
Barcelona za ta fita daga filin wasa na Nou Camp a kakar wasanni mai zuwa, don ta ba da damar sake gyara shi.
Amma magoya bayan ƙungiyar za su samu damar yin murnar lashe wannan babban kofi tun kakar wasa ta 2020-21 a lokacin wasanni biyu da za su buga na ƙarshe a gida, na farko da Real Sociedad a ranar Asabar, sai kuma karawa da Mallorca ranar 28 ga Mayu.
No comments