Daga Ammar M. Rajab Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr (Mrs) Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin sabuwar Aka...
Daga Ammar M. Rajab
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Dr (Mrs) Oluwatoyin Sakirat Madein a matsayin sabuwar Akanta Janar na kasa biyo bayan tantance masu neman mukamin.
Hakan ya fito ne a wata takarda da ofishin shugabar ma'aikata na gwamnatin Tarayya ta fitar dauke da sa hannun Daraktan sadarwa na ofishin, Mohammed Abdullahi Ahmed.
Takardar mai dauke da kwanan wata 19 ga watan Mayun 2023 wanda jaridar MADOGARA ta gani, ta ce shugabar ofishin, Dr Folasade Yemi-Esan ita ce ta tabbatar da hakan a yau Juma'a a Abuja, inda ta ce nadin ya soma aiki ne a ranar Alhamis 18 ga watan Mayun 2023.
Sanarwar ta ce sabuwar mai rike da mukamin ta soma aiki nan take.
No comments