Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Doguwa Ya Ƙaddamar Da Neman Shugabancin Majalisar Wakilai Ta 10

  Shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai ya ce duk mutumin da zai iya riƙe mata huɗu da 'ya'ya 28 kamar shi, zai iya neman shugab...

 


Shugaban masu rinjaye a Majalisar Wakilai ya ce duk mutumin da zai iya riƙe mata huɗu da 'ya'ya 28 kamar shi, zai iya neman shugabancin majalisar wakilai zango na goma.

Alhassan Ado Doguwa ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba lokacin da a ƙa'idance yake sanar da aniyarsa ta neman kujerar mutum na huɗu mafi girman muƙami a Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito wata sanarwa daga shugaban masu rinjayen wadda a ciki yake mayar da martani gamasu cewa ba shi da ƙwarewa da kuma taushin halin da zai iya maye gurbin shugaban majalisa na yanzu saboda irin halayyarsa.

Ya ce, “Ko lokacin da na zama Mai Tsawatarwa a Majalisar Wakilai, ban taɓa nuna zafin rai ba. Ga masu cewa ni mutum ne mai zafin zuciya, sun yi kuskure don ba su san wane ne Ado Doguwa ba, mutumin da yake da mata huɗu da 'ya'ya 28. Ban taɓa sakin mace ba. Haka kuwa manuniya ce cewa ina da abin da ake neman ga mutumin da zai yi fice a matsayin shugaban majalisar wakilai na gaba".

A cewarsa “ga mutum kamar ni wanda ya kasance a majalisa tun daga 4 ga watan Yulin 1992, zuwa yau kuma cikin nasara ya smau damar wakilcin jama'ata.

Ɗan majalisar wanda ke wakiltar mazaɓar Doguwa/Tudun Wada daga Kano a yanzu haka yana fuskantar shari'a bisa zargin haɗa baki don aikata laifi da aikata kisan kai da mallakar bindiga ta haramtacciyar hanya da tayar da hankulan jama'a.



No comments