Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

El-Rufai Ya Bi Dare Ya Rushe Asibiti, Makarantu Da Gidajen Al’umma A Kaduna

Daga Muhammad A. Dalhatu, Kaduna Kasa da kwana takwas da barin mulkin jihar Kaduna, Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya bada umurnin ...


Daga Muhammad A. Dalhatu, Kaduna

Kasa da kwana takwas da barin mulkin jihar Kaduna, Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya bada umurnin rushe asibiti, makarantu da kuma gidajen al’umma a jihar Kaduna.

Rahotannin da suka shigowa Jaridar MADOGARA na nuni da cewa da misalin karfe 1:30 na daren ranar Lahadi 21 ga watan Mayun 2023, tawagar hukumar tsara birane ta jihar Kaduna, wato KASUPDA ta rushe asibitin Kauthar da aka gina domin al’umma da makarantun Fudiyya dake Rimi, Danmadami, Tudun Wada, da Gidan Alhaji Musa Birnin Yero.

Wasu ganau sun shaidawa wakilinmu cewa jami'an rushe muhallan sun tattake Alkur'ani mai girma tare da rushe gine-ginen kan Alkur'anan. 
KASUPDA ba su bayar da wani notis ko dalilin rushe muhallan ba kamar yadda Muhammad Rabiu ya shaidawa wakilinmu a Kaduna. 

Idan ba ku manta ba, kafafen watsa labaran Nijeriya sun labarto cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya amince da rushe muhallan wadanda ya kira da ‘IMN’ da kuma wasu gine-gine dake Gbagyi da wadansu wurare duk a jihar ta Kaduna kasa da mako 2 ya kammala mulkinsa a jihar ta Kaduna. 

El-Rufai ya amince da rushe wadannan muhallai ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 20 ga Afrilun 2023. Inda hukumar KASUPDA ke neman naira 29,253,500 da kuma jami'an tsaro sama da dubu biyu domin gudanar da wannan aikin rushe-rushen.

Cikin adadin wannan kudin, hukumar ta KASUPDA na da bukatar N20,253,500 domin rushe muhallan da ya kira na ‘IMN’.

Sai dai a wata takardar karar da aka shigar a gaban babbar kotun Kaduna mai dauke da lamba KDH/KAD/515/23; makarantun Imam Sadiq Academy LTD, Tahfiz Fudiyyah Zaria, Fudiyyah Nursery and Primary Schs., Saminu Kusa Muhammed, Ahmad Abubakar, Haruna Danfulani U/Mu’azu, Shuhada Foundation,  a madadinsu da kuma ‘Yan Shi’a mazauna jihar Kaduna sun maka gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Gwamnatin jihar Kaduna, Ma’aikatar Gidaje da ci gaban Birane ta jihar Kaduna, KASUPDA, da kuma Daraktan KASUPDA, Isma’il Umaru Dikko a gaban kotun ne bisa yunkurin da suke yi na rusa musu muhallai ba bisa ka’ida ba da kuma sunan cewa na ‘IMN’ ne.

Masu shigar da karar sun ce wadannan muhallai ba su da alaka ta kusa ko ta nesa da abin da wadanda aka maka gaban kotun suke ikirari. Inda suka nemi kotun da ta dakatar da su.  

Karar wanda aka shigar a gaban babbar kotun jihar Kaduna, har wala yau kara neman da kotun ta bayar da umurnin hana rushe musu muhallai da sunan cewa na ‘IMN’ ne. Inda suka ce gine-ginensu ne da suka gina bisa ka’idar doka, kuma suna da dukkanin wani shaida na yin gini a jihar ta Kaduna. 

Sannan sun kuma nemi kotun da ta ci tarar wadanda ake kara inda aka same su da wannan laifi bisa wannan yunkuri da suka yin a rusa musu muhallai. 

Wakilinmu ya shaidi shaidar shigar da karar wacce aka gabatar a gaban babbar kotun na Kaduna  dauke da kwanan wata 18 ga watan Mayun 2023. 

No comments