Daga Hagu: Kwamared Aminu Abdussalam tare da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo Zababben mataimakin gwamnan jihar K...
Zababben mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam, ya bayyana wanda ya kafa rukunonin jami’o’in Maryam Abacha American University ta Nijeriya da Nijer da kuma Franco-British University dake Kaduna da Canadian University a Abuja, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a matsayin ɗan albarka a dukkanin ma’aunin da ka sanya shi.
Kwamared Abdussalam ya bayyana hakan ne a taron cin abinci da kungiyar tuntuba ta Gwarzo wato Gwarzo Consultative Forum ta shirya a ranar Asabar a Otel din Bristol Palace dake Kano.
Kwamared Abdussalam ya ce ko shakka babu Farfesa Gwarzo ɗan albarka ne; “Ina godiya mai tarin yawa ga wannan da namu Farfesa Adamu. Ko shakka babu Farfesa duk ma’aunin da ka sanya shi sunansa ɗan albarka. Muna alfahari da shi. Muna jinjina masa a matsayinsa da shekarunsa yadda yake ratsa duk duniya ya yi fafutika ya taho ya kawo ƙasarsa, ya taso jiharsa, kuma bai manta da ƙaramar hukumarsa ba. Muna gode masa irin ɗawainiyya da gudummawa da yake bayarwa a bangaren ilimi a tarayyar Nijeriya, a jihar Kano da karamar hukumarsa”, inji shi.
Dangane da irin gudummawar da Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo yake bai wa bangaren ilimi da hadin kai tare da kawo ci gaba, Kwamared Abdussalam bai manta da hakan ba, inda ya nuna jindadinsa da godiyarsa bisa hakan, inda ya ce; “Irin yadda ka tsaya sosai a kan duk wani abu na hadin kai da ci gaba. Jami’a ya kafa ita kanta da sunan karamar hukumar Gwarzo ya yi Rajistar wannan Jami’ar. Kawai dai lalura ce ya sa yanzu tana nan a karamar hukumar Nasarawa cikin birnin Kano. Can ma ya bude bangare an kewaye za a fara aiki kowanne lokaci daga yanzu. Muna yi maka godiya kwarai da gaske, muna addu’a ita ma wannan Jami’ar ko reshenta da za ka sanya mana a Gwarzo muna fatan cikin ‘yan lokutan nan ba da nisa ba mu ga aiki ya kankama. Burinmu ke nan kuma za mu baka dukkanin goyon bayan da yakamata insha Allahu ta’ala”.
Da yake tsokaci dangane da taron da aka shirya, Kwamared Abdussalam ya ce lallai al’ummar karamar hukumar Gwarzo, sun ci, sun sha a taron, kuma sun godewa Allah da irin baiwar da ya yi wa Farfesa Gwarzo.
“Muna gode masa da damuwa da damuwar al’ummar karamar hukumarsa. Ko shakka babu, Farfesa ya bamu gagarumar gudummawa a fannoni daban-daban, a ciki harda wannan siyasar da muke yi. Muna gode masa, muna yi masa addu’a Allah ya kara masa fikira, Allah ya kara masa daukaka. Allah ya kara yaukaka arzikinsa”, ya nusasshe.
Ya kuma mika sakon godiyarsa ga kafatanin wadanda suka samu damar halartar taron da wadanda suka aiko da uzurin rashin halartar taron, inda ya ce “jama’a muna godiya ga dukkanin wanda ya samu halartar wannan taro mai albarka. Muna gode ma wadanda ba su ma samun damar zuwa ba suka aiko da uzuri da ya hana ba za su samu damar zuwa ba. Da wadanda yanayi da yadda za a yi taron ba zai yiwu a bude kowa ya zo nan ba, suna nan suna fatan alheri, wasu ma suna makagin ba a gayyace su ba, su yi hakuri saboda irin wannan tabbas wani ya zo, wani kuma ba za a samu a gayyace shi ba, don ba za a iya yi da kowa da kowa ba. Wakilci ne alhamdulillahi an samu wakilci. Kuma mungode kwarai da gaske, Allah ya sakawa dukkan wadanda suka bada uzuri ba su samu zuwa ba, da wadanda suka zo suma Allah ya saka musu da alheri. Kuma muna fata Allah ya maida kowa gidansa lafiya”, ya yi addu’a.
A karshe ya yi godiya ga kungiyar Gwarzo Consultative Forum bisa wannan kokari, inda ya kara da cewa; “muna kara jaddada godiya a gare ku, da fatan ka da Allah ya gajiyar da ku”.
No comments