BBC Hausa sun labarto cewa; Hukumar kula da ingancin abinci a Nijeriya wato NAFDAC, ta ce tana gudanar da bincike kan taliyar k...
BBC Hausa sun labarto cewa; Hukumar kula da ingancin abinci a Nijeriya wato NAFDAC, ta ce tana gudanar da bincike kan taliyar kamfanin Indomie da ƙasashen Taiwan da Malaysia ke samarwa, bayan gano sinadarin Ethylene Oxide da ke haddasa cutar kansa a cikin ta.
Shugabar hukumar ta NAFDAC, Mojisola Adeyeye ta ce kawo yanzu jami’an hukumar da ke kula da dakin gwaje-gwajen na ingancin abinci sun dukufa wajen bin matakai na faÉ—aÉ—a bincike kan sinadarin.
Ya zuwa hada wannan rahoton babu sakamakon binciken hukumar a hukumance, sai dai ta ce tuni dama ta haramta shigo da taliyar a kasar tare da dakile hanyar shigo da ita ta barauniyyar hanya.
No comments